2019: Gwamnan Neja Ya Musanta Rahotannin Canjin Sheka — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

2019: Gwamnan Neja Ya Musanta Rahotannin Canjin Sheka

Published

on


Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya musanta rahotannin da ake yadawa na shirin barin jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Rahotannin dai sun taso ne a lokacin da wasu gwamnoni da ‘yan majalisun tarayyar ke rububin barin jam’iyya mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP. Gwamnan ya ce, yana nan daram a cikin jam’iyyar APC domin ya gamsu da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar ke gudanar da ayyukanta.

Gwamnan ya ce, shi a jam’iyyar APC ba mamba ba ne kawai, daya ne daga cikin ginshikan da suka taka rawar ganin jam’iyyar ta kafu kuma ta ceto kasar nan daga hannun gwamnatocin da suka gabata.

Shekaru uku da suka gabata mun tsaya tsayin daka wajen kawo ingantattun manufofin inganta harkar aikin gona da ilimi da tsaro da inganta rayuwar matasa da farfado da tattalin arzikin kasa.

Mun mayar da hankali kan kammala ayyukan da gwamnatocin baya suka faro ba a kammala ba ta yadda zamu tabbatar wa al’ummar jiha cewar gwamnatin mu gwamnati ce ta ci gaba da hadin kai da ci gaban kasa.

Gwamnan ya ce, gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi bajinta wajen ayyukan ci gaban kasa da ya kamata a mara wa baya don ganin ta kammala ayyukan alheri da ta sanya a gaba dan inganta da dawo da martabarta a idon duniya.

Gwamnan ya ce, gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu nasarar kammala aikin madatsar ruwa Baro da aikin tagwayen hanya wanda ya tashi daga Minna zuwa Suleja da aikin hanyar Bida zuwa Lapai da ta wuce Agaie zuwa Lambata. Da kuma gyara gadar Kutigi zuwa Mokwa da ma wasu ayyukan da dama.

Dan haka mai girma Muhammadu Buhari yana da kyakkyawan manufar da zamu ba shi hadin kai da goyon baya ta yadda zai samu nasarar kammala manufofin sa na yaki da rashawa, farfado da tattalin arzikin kasa da samar da ingantaccen tsaro a kasa.

Advertisement
Click to comment

labarai