Mazauna Gidajen Yarin Kano Na Samun Horon Sana’o’i Daban Daban — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Mazauna Gidajen Yarin Kano Na Samun Horon Sana’o’i Daban Daban

Published

on


Gidajen yari wuri ne na gyara tarabiya tare da tabbatar da samun horo ingantacce, wannan tasa Kwanturolan Gidajen Yarin da ke Jihar Alhaji Abdullahi Magaji mayar da hankali wajen tabbatar da ganin mazauna gidajen yarin da ke karkashin kulawarsa na samu kyakkyawan horo kan sana’u da kuma harkokin ilimi domin ganin duk lokacin da suka fita daga wannan gida zasu zama mutanen kirki wadanda zasu ci gaba da gudanar da sana’un da suka koya alokacin zamansu a gidan yari.

Kakakin Hukumar dake lura da gidajen yari a Jihar Kano Malam Musbahu ya bayyanawa wakilinmu cewar Kwanturolan gidajen yarin na Jihar Kano na daukar duk wani wanda Kaddara ta kawo shi wannan gida kamar dan da ya Haifa, musamman wajen tabbatar da ganin kowa na samu cikakken abinci, kulawa da lafiya da kuma koyar da daurarrun sana’u iri daban daban. Malam Musbahu ya ci gaba da cewa Kwanturola Alhaji Abdullahi Magaji ba ya iyar runtsawa har sai ya samu cikakken rahoton cewa gidajen yarin na cikin kwanciyar hankali.

Bangaren mata daurarru na cikin wuraren dake zaman zakaran kwajin dafi ta fuskar koyar da sana’u, wanda yanzu haka akwai mata da yawa wadanda suka iya sarrafa sarkokin wuya da ‘yan kunne, ga kuma wadanda aka koyawa yadda ake yin sabulai da turarukan shafawa domin kwalliyar mata, wannan tasa muke da kyakkyawan zaton idan ire iren wadannan mata suka gama zaman lokacin da aka dibar masu, da sun koma cikin iyalansu zasu zama cikakkun mutane masu dogaro da kansu, wanda kuma da yawa rashin sana’a ne ya zama sanadiyyar shigar su wannan gida.

Hakazalika a cikin kokarin da shugaban Hukumar gidajen yari na kasa ke yi na  tabbatar da rage cinkosu a gidajen yarin kasar nan, yanzu haka aiki ya yi nisa na samar da sabbin wuraren aje daurarru a gidan yarin Kurmawa, baya ga zagaye wasu gidajen yarin da ake tayi a Jihar Kano a halin yanzu. Sai kuma tabbatar da kyakkyawar danganta ka tsakanin shugaban hukumar gidajen yarin Jihar Kano da sauran ma’aikata, wanda yanzu kowane ma’aikaci ke samun damar  gudanar da ayyukansa cikin nishidi da kwanciyar hankali.

Da yake tsokaci kan irin gudunmawar da Gwamnatin Jihar Kano ke bayarwa ga Gidajen yarin jihar Kano, Alhaji Abdullahi Magaji ya bayyana gamsuwa tare jinjinawa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa aniyarsa ta inganta rayuwar daurarru domin samun ingantacciyar al’umma nan bada jimawa ba, ya ce kwanan nan ‘Yan majalisar Dokokin Jihar Kano suka kawo ziyara gidajen yari inda suka ganewa idonsu halin da ake ciki, wannan tasa yanzu haka akwai kyakkyawan tanadin da suke shirin samarwa wadanan gidajen yari a Jihar Kano domin tabbatar da cigaban da ake bukata.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!