Saraki Ya Ziyarci IBB A Minna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Saraki Ya Ziyarci IBB A Minna

Published

on


Shugaban Majalisar Dattawa ya isa garin Minna don wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, wato Janar Ibrahim Babangida a gidan shi dake Minna.

Sarakin ya sauka ne da misalin karfe hudu na yammacin yau a filin sauka da tashin jiragen sama dake Minna, inda daga nan ya zarce gidan tsohon shugaban, ba a san dai akan mai za su yi tattaunawar ba, wasu na ganin Sarakin yana sha’awar fitowa takarar shugabancin kasa, kuma akan wannan ne ma ya ziyarci tsohon Sojan.

Yayin da aka tambaye shi ko zai sauka daga shugabancin majalisar dattawa sai yace: mukamin nan ba bani aka yi ba, zaba ta akayi, kuma doka ta ba kowanne Sanata damar tsayawa takarar shugabancin majalisar ba tare da la’akari da dan wacce jam’iyya bane shi.

Advertisement
Click to comment

labarai