An Bubaci Al’ummar Kano Su Tabbatar Da Karbar Katin Zabe — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

An Bubaci Al’ummar Kano Su Tabbatar Da Karbar Katin Zabe

Published

on


Mataimakin Shugaban Bungiyar Shugabannin Bananan hukumomi na jihar Kano.ALGON.Shugaban Baramar Hukumar Bichi.Barden Bichi.Alhaji Sani Mubaddas ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su yi bobari su mallaki katin zabe dana zama danbasa da ake yi a halin yanzu domin kare yancinsu da mutuncin jihar kano.

Ya ce katin zaben yana da mutubar muhimmanci ga al’umma wanda da shi ne za su sami dama su tabbatar da shugabanni da za su kawo musu ci gaban rayuwarsu.

Alhaji Sani Mubaddas  ya bara da cewa irin aikin da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje  yake da shi  na ganin an wayar da kan  al’ummar jihar Kano na shirya gangami na musamman a gidan Gwamnati daya hada dukkan masu ruwa da tsaki na Kano da sauran al’umma da wayar da kai a kan muhimmancin karbar katunan.

Mataimakin Shugaban ALGON na jihar Kano Alhaji Sani Mubaddas ya yi nuni da cewa a yanzu haka da zabuka ke gabatowa  a basarnan  ya zama wajibi a matsayinsu na shugabanni  su ja hankalin jama’a  a kan suje su karbi wannan katin duba da cewa jihar Kano Allah ya albarkaceta da dinbin al’umma fiye da  kowace jiha a basar nan.

Ya ce  idan al’umma suka sake basu sami wadannan katuna ba yawan zai zama mara amfani ga ci gaban jihar nan. Dan haka yin katin zai taimakawa jihar Kano ta tabbatar da matsayinta na kan gaba a yawan jama’a a basar na  kuma yawan ya yi anfani wajen  ci gaban jihar nan.

Alhaji Sani Mubaddas ya ce a matsayinsu na shugabanin bananan hukumomi a jihar Kano sunan bobari a yankunan bananan hukumominsu ta wayar da kan mutane game da muhimmancin karbar katin zabe dana dan basa kuma suna ba da duk wata gudummuwa daya kamata domin tabbatar da nasarar karbar katin.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!