An Bubaci Gwamnati Ta Hukunta Masu Shigo Da Kayan Gyaran Mota Na Jabu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

An Bubaci Gwamnati Ta Hukunta Masu Shigo Da Kayan Gyaran Mota Na Jabu

Published

on


Masu ruwa da tsaki a fannin sufuri dake cikin jihar Legas, sunyi kira ga gwamnati data tabbatar da masu direbobin sufuri suna  bin ba’idojin hanya da kuma hukunta masu sufurin da suke shigo da kayan mota marasa inganci da kuma sanya ido akan sauran motocin gudanar da sufuri da suke shigowa cikin jihar daga sauran jihohin dake basar nan. Sun yi kiran ne a lokacin wani taron kwana daya da hukumar duba ababen hawa BIS tare da hadin gwiwar hukumar binciken ababen hawa ta jihar LACBIS suka shirya wanda ya a gudana a Gbagada, inda masu ruwan da tsaki sukace, matakin zai taimaka wajen ci gaba da aukuwar hadurra akan titunan jihar. Masu ruwan da tsaki sun hada da, bungiyoyin NUPENG, AMATO, PTD, NATO,CTOAN da kuma sauransu. A jawabinsa na maraba  Janar Manaja na LACBIS Mista  Segun Ogunnaike ya ce, taron yana da mahimmanci musamman don a fadakar da masu ruwan da tsakin a fannin akan abinda gwamnatin jihar ta birbiro don magance hadurra a titunan jihar ya kuma yi kira a gare su dasu tabbatar da samar da cin nasarar shirin na gwamnatin jihar.  Mista Ogunnaike ya kuma bayyana cewar, an kuma kafa cibiyoyi goma na duba lafiyar ababen hawa a daukacin fadin jihar don a samu su kai guda hamsin nan da shekaru uku masu zuwa. Shima a nashi jawabin Daraktan duba ababen hawa na hukumar BIS Injiniya  A.G. Toriola, ya sanar da cewar jihar tuni ta daina yin amfani da hanyar gargajiya ta duba ababen hawa a jihar, inda aka cike makwafin hakan da na’urar zamani kamar yadda ake yi a duniya. Ya kuma yi kira ga masu ruwan da tsaki dasu yi hadaka da gwamnatin jihar don rage hadurra a titunan jihar. Mosumola Samuel wadda ta wakilci hukumar kula da ingancin kaya ta basa SON ta yi nuni da cewar, za’a iya rage haddura ne kawai idan masu ruwa da tsaki suna bin ba’ida wajen yin amfani da kaya masu inganci da hukumar ta gindaya. Shi ma wakilin bungiyar Inshora ta basa Mista Soji Oni, ya ayyana budurin bungiyar na yin hadaka da masu ruwan da tsaki don rage haddura a basar nan. Shi kuwa Daraktan BIS na sashen cibiyar koyon tubi a jihar Mista Akin-George Fashola dasu rungumi cibiyar don rage hadurra a titunan jihar kuma yayan bungiyoyin su dinga tabbatar da suna karbar lasisin tubi wanda aka amince da shi.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai