Arsenal Tana Neman Dembele — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Arsenal Tana Neman Dembele

Published

on


Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ousman Dembele, dan kasar Faransa wanda kungiyar takeson siyarwa.

Dembele, ya koma kungiyar Barcelona ne daga kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund a kakar wasan data gabata sai dai tun bayan komawarsa kungiyar yafara fama da ciwo wanda yasa sai da yayi watanni hudu yana jiyya bayan anyi masa tiyata.

A kwanakin baya an danganta dan wasan da komawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea sai dai daga baya kuma kungiyar ta Chelsea tace bata zawarcin dan wasan bayan da tace bazata siyar da dan wasanta Hazard ba ga kungiyar Real Madrid.

Dembele dai wakilci kasarsa ta Faransa a gasar cin kofin duniyar da suka lashe a kasar Rasha sai dai wasanni biyu kacal aka fara da dan wasan wanda Barcelona ta biya fam miliyan 97 a lokacin data siyeshi.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai tana da burin daukar dan wasan amma kuma a matsayin aro da sharadin za ta siyi dan wasan a kakar wasa mai zuwa idan har tauraruwarsa ta haska a gasar ta firimiya ta bana.

A kwanakin baya ma dai an danganta dan wasan da komawa manchester United bayan da kungiyar itama take neman wanda zai maye mata gurbin Anthonio Martial wanda shima yake da niyyar barin kungiyar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai