Bakayoko Yana Dab Da Komawa Ac Millan A Matsayin Aro — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Bakayoko Yana Dab Da Komawa Ac Millan A Matsayin Aro

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta AC Millan dake kasar Italiya tana dab da kammala amincewa da daukar dan wasan tsakiyar Chelsea, Bakayoko a matsayin aro bayan da sabon kociyan kungiyar ya bayyana cewa bazaiyi amfani da dan wasan ba.

Bakayoko wanda yakoma Chelsea daga kungiyar kwallon kafa ta Monaco dake kasar Faransa a kakar wasan data gabata akan kudi fam miliyan 41 ya buga wasanni da dama a kungiyar ta Chelsea karakashin mai koyarwa Antonio Conte.

Dan wasan mai shekaru 23 a duniya ya bayyana cewa yanason cigaba da zama a kungiyar domin neman wajensa sai dai mai koyar da kungiyar ya ce masa baya bukatar salon yadda yake buga wasa saboda haka baya bukatarsa.

Tun farko dai Kungiyar kwallon kafa ta AC Millan tafara neman dan wasa Sergej Milinkobic-Sabic ne daga kungiyar Lazio sai dai Lazio ta bayyana cewa dan wasan na ta bana siyarwa bane hakan yasa suka koma neman Bakayoko.

Chelsea dai tana son siyar da dan wasanne sai dai kungiyar kwallon kafa ta AC Millan tafison karbar aron dan wasan yayinda daga baya kuma za ta biya kudinsa idan har ya buga abinda akeso a kungiyar.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Lyon dake kasar Faransa tana zawarcin dan wasan a matsayin aro bayan da Chelsea take zawarcin dan wasan kungiyar Nebil Fekir wanda shima dan kasar faransa ne.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!