Gwamanatin Borno Ta Daukin Nauyin Karatun Israel Galadima — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamanatin Borno Ta Daukin Nauyin Karatun Israel Galadima

Published

on


Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bayar da umurnin baiwa dalibin da ya zo na daya a jarabawar share-fagen shiga jami’a ta basa (JAMB); Israel Galadima tallafin karatu na shekara biyar, a jami’ar ‘Cobenant Unibersity’ da ke jihar Ogun.

Dalibi Israel Galadima Zakari haifaffen Biu ta jihar Borno, wanda hukumar tsara daukar jarabawar ta ayyana a matsayin wanda ya zo na daya a fadin Nijeriya, da maki 364, a jarabawar da JAMB ta shirya a wannan shekara ta 2018.

Gwamna Shettima ya bayyana hakan ne a yau Laraba (jiya), a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a lokacin da yake ganawar musamman da dalibin; tare da mahaifiyar Zakari Galadima, Jummai. Ya ce biya wa dalibin kudin tallafin karatun kai tsaye, saboda gudun ko da ya bar ofis a shekara mai zuwa, iyalan dalibin su sha wahalar je ka dawo.

Bugu da bari kuma, Gwamna Kashim Shettima ya umurci kwamishinan ilimi mai zurfi a jihar Borno, Usman Jaha, ya rubuta cak na naira miliyan biyar (N5m) domin biya wa dalibin kudin makaranta, littafai, tare da na dakin kwana, a jami’ar ‘Cobenant Unibersity’ da ke jihar Ogun inda dalibin ya samu makaranta domin karanta Digiri a fannin ‘Electronics Engineering’.

“Israel, kamar yadda mahaifiyar sa ta bayyana muna, ya taso a matsayin maraya, wanda ta ce mahaifin sa mai mubamin Manjo a sojan Nijeriya, ya rasu tun a shekaru 14 da suka, inda ya barta da yara uku, wanda Israel shi ne dan ta na biyu”.

“ta kasance ta na aikin banki a Legas, saboda haka bama son ta sake fita shan wahalar kai komo na nema wa wannan yaro kudin makaranta-daga Maiduguri. Ita ta riga ta gama nata aikin, tunda da ta samar mana da hazibin yaro wanda jihar Borno zata yi alfahari da shi”.

“wanda haka wajibi ne a gare mu wajen taimaka masa. Bisa ga wannan ne muka yanke shawarar biya masa kudin karatu, baki daya saboda gudun barin kudin zuwa nan gaba. Ina mai matubar baunar Israel saboda yadda ya daga martabar marayu.” Inji Shettima.

Mahaifiyar dalibi Israel, Jummai, wadda take cike da fara’a tare da jin dadi, ya yaba matuba dangane da girmamawar da Gwamna Shettima ya yiwa iyalan ta, wanda ta bayyana lamarin da cewa “abin ya wuce tunanin mu”.

“Ya Maigirma Gwamna, tun bayan rasuwar maigida na, ban yi sakaci ba wajen kulawa da wadannan yara nawa su uku. Ni ma’aikaciyar banki ce a Legas kuma Israel yana da yaya da take karatu a jami’a.

“amma a cikin wannan jinbai naka wanda ya zarta tsammanin mu, ka daga darajar mu. Domin a habibanin gaskiya, a lokacin da sabon ka na gayyata kan cewa kana son ganina tare da dana, ban yi tunanin wannan babbar kyauta irin haka da ka bamu ba”. inji ta.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!