INEC: Kashi Saba’in Ne Suka Kasa Amsar Katin Zabensu A Neja — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

INEC: Kashi Saba’in Ne Suka Kasa Amsar Katin Zabensu A Neja

Published

on


An tabbatar wa ma’aikatan hukumar zabe cewa hukumar za ta basu hadin kai dan ganin aikin ya inganta, shugaban hukumar zabe ta basa a jihar Neja, Farfesa Samuel Ego ne ta bada tabbacin jiya laraba da ya kira taron manema labarai a sakatariyar hukumar.

Farfesa Egu ya cigaba da cewar yanzu haka hukumarta ta sabunta rajistan masu zabe wadanda suka canja madauninsu a ballan su dubu shida amma kashi daya ne kawai suka iya karban katin su.

Hukumar ta bada tabbacin cewar 17 ga watan Augustan nan hukumar za ta dakatar aikin sabunta katin masu zabe bisa wasu dalilai, domin kamar doka tace za a dakatar da aikin ne kwana sittin  kafin zabe amma saboda zabukan cika gurbi da za a gudanar a jahohin Bauchi da Katsina ne ya tilas hukumar ta dakatar da aikin baki daya domin fuskantar wadannan zabukan masu zuwa.

Farfesa Egu ya ce a shekarar nan kawai mutane 93,0208 suka sabunta rajistansu wadanda suka canja mazaunai da wadanda suka kai lokacin mallakar katin zaben, yanzu haka hukumar ta buga kati 82,896 wanda duk suna hannun masu shi, kafin wa’adin zabe kowa zai samu katinsa a hannun sa. Yanzu a shekarar 2018, 198,038 ne suka sabunta rajistan su wanda hakan na nuna wadanda suke karban katin sun dara shekarar 2017.

Shugaban ya ce yanzu haka suna fuskantar matsaloli musamman na rashin karban katin ga wadanda suka bubata, ya ce ma’aikatan sa za su aiki a tabaitaccen lokaci har da lokuttan hutun barshen mako dan ganin katin ya isa ga masu shi. Hukumar ta nemi duk wadanda suka sabunta katunansu da su gaggauta zuwa cibiyoyin da suka yi rajistan dan karban katin su.

Shugaban hukumar ya jawo hankalin jama’a da ke borafin ana karban kudade a hannun su kafin a sabunta masu katin, da cewar hukumar ba ta san da wannan ba amma wajibi jama’a su taimakawa wajen fadakar da jama’a muhimmancin karban katin da anfaninsa gare su.

Domin ita hukumar aikin samar da kayan aikin zabe da kula da yadda zabukan zasu kasance, ba zamu amince wani karbi katin wani ba domin ba zai jefa buri’a ba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai