Kroenke Zai Sayi Arsenal Gaba Dayanta — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Kroenke Zai Sayi Arsenal Gaba Dayanta

Published

on


Shahararren Attajirin nan na Amurka da ya fi kowa hannun jari a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, wato Stan Kroenke ya gabatar da bukatar siye kungiyar baki daya don zama mallakarsa shi kadai.

Rahotanni na cewa, yarjejeniyar siye kungiyar za ta lakume kimanin Pam biliyan 1 da miliyan 800, kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 300

Da ma dai attajirin ya mallaki kashi 67 cikin 100 na hannun jarin Arsenal ta hannun kamfaninsa KSE, yayin da kuma Alisher Usmanob na Rasha ya amince da ya siyar ma sa da kashi 30 da ke karkashin mallakarsa.

Kroenke ya yi amanna cewa, mallakar kungiyar a karkashin mutun guda, za ta taimaka wajen ci gaban kungiyar ta Arsenal.

Kroenke shi ne mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles Rams da ke Amurka, yayin da ya fara zuba jari a Arsenal a shekarar 2007, in da kuma yake ci gaba da kara jarinsa kadan-kadan.

Advertisement
Click to comment

labarai