Kwankwaso Da Sanatoci 46 Sun Sa Hannu Kan Takardar Goyon Bayan Saraki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kwankwaso Da Sanatoci 46 Sun Sa Hannu Kan Takardar Goyon Bayan Saraki

Published

on


Tsohon Shugaban majalisar Dattawa, Dabid Mark, da Sanata Jonah Jang, Abiodun Olujimi da Rabi’u Musa Kwankwaso, suna cikin ‘yan majalisar Dattawa 49 da suka sanya hannu kan bin amincewa da duk wani yunburi na neman tilasta kawo wani sauyi a cikin shugabancin majalisar ta dattawa.

An ce, an sanya hannun ne domin ya zama gargadi ga wadanda suka yi yunburin da bai yi nasara ba na tsige shugaban majalisar ta dattawa, Bukola Saraki, da mataimakinsa Ike Ikweremadu.

Wadanda suka sanya hannun, wanda yawancin su ‘yan Jam’iyyar PDP ne, an dauki sunayen na su ne a farfajiyar shiga majalisar.

Jerin sunayen wanda wakilinmu ya tsinkayo shi yana cewa, “Mu Sanatocin da sunayenmu ke cikin wannan takardan, muna shelanta wa duniya cikakkiyar biyayyan mu ga Sanata Bukola Saraki da Ike Ekweremadu, a matsayin su na shugaba da kuma mataimakin wannan majalisa ta Dattawa ta Nijeriya. Kuma ba mu tare da duk wani yunburi na barya domin tsige su da wasu ‘yan tsiraru suke yi.”

In za a iya tunawa, an yada jita-jitan cewa wasu Sanatoci na Jam’iyyar APC sun yi wani yunburi na aukowa majalisar domin su taru su kuma canza shugababnin majalisar, wanda hakan ya sanya wasu Sanatocin na Jam’iyyar PDP suka yanke hutun da suke yi domin su zo su watsa wannan aniyar ta su.

Sai dai, lokacin da Sanatocin na PDP suka iso majalisar wasu jami’an tsaro daga hukumar SSS, da suka rufe fuskokin su, sun hana su shiga harabar majalisar, inda suka shaida ma Sanatocin cewa daga sama ne aka ba su umurnin su hana su shiga majalisar.

Advertisement
Click to comment

labarai