Madrid Ta Siya Mai Tsaron Ragar Chelsea Courtouis — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Madrid Ta Siya Mai Tsaron Ragar Chelsea Courtouis

Published

on


Rahotanni daga kasar Belgium sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thibaut Courtois yana gab da kammala komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a yau idan har kungiyoyin biyu sun kammala yarjejeniya.

Courtois, mai shekara 25 a duniya ya bayyana karara cewa yana bukatar komawa kasar Sipaniya domin komawa kusa da iyalansa yaci gaba da buga wasa bayan da tun zamansa a `kasar Sipaniya iyalan nasa suke zaune a Sipaniya.

Dan wasan dai ya shafe kwanaki biyu baya halartar filin daukar horo na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a kokarin da yakeyi na barin kungiyar domin cikar burinsa na bugawa Real Madrid wasa a kakar wasa mai zuwa.

Mai tsaron ragar dai ya bayyana cewa yanason barin kungiyar Chelsea a kakar wasannan sai dai shima sabon kociyan kungiyar, Mauricio Sarri ya bayyana cewa bazai hana dan wasan barin kungiyar ba idan har kungiyar tace zata siyar dashi.

Rahotanni sun bayyana cewa ana saran yau za’a iya kammala cinikin mai tsaron ragar bayan da har yanzu bai koma kungiyar tasa ba domin fara shirin kakar wasa mai zuwa wadda za’a fara a wannan satin.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dai tuni ta bazama wajen neman wanda zai maye mata gurbinsa bayan data nemi mai tsaron ragar kungiyar Atletico Bilbao, Kepa, wanda ake saran shine kungiyar zata siya.

Advertisement
Click to comment

labarai