Musulmi Da Kiristoci Sun Shirya Taron Fahimtar Juna A Adamawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Musulmi Da Kiristoci Sun Shirya Taron Fahimtar Juna A Adamawa

Published

on


Matasa barbashin Dandalin Matasa na Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN), sun shirya taron fahimta da kusantar juna tsakanin matasan musulmi da kirista a jihar Adamawa.

Taron wanda shine karo na hudu da matasan ke shiryawa ya samu halartan matasan musulmi da kiristocin ya gudana ne albarkacin zagayowar ranar Maulidin Annabi Isa (as), da dama matasan kan shirya duk shekara.

Da yake jawabi a taron shugaban reshen matasa na bungiyar kiristoci ta basa (CAN) a jihar Adamawa Ajino Dalon, ya nuna farin  ciki da shirya taron, ya ce duk da ba shine halartarsa taron na farko ba, ya halarta ne domin muhimmancinsa.

Ya ce “wannan taro yana muhimmanci kwarai da gaske, saboda matasa sune masu gyarawa sune kuma masu batawa, idan sun gyara ya gyaru.

“ bai kamata mu yadda banbancin addini ko harshe ya riba kawo mana matsala ba, dole ne mu martaba juna, mu yiwa juna ahuwa, yiwa juna ahuwa yiwa Allah Ubangiji ibada ne.

Shugaban matasan bungiyar kirstocin ya kuma gargadi matasa da cewa bai kamata su riba daukan magana haka siddan “muddin matasa basu bar daukan magana haka kawai ba, to ba za’a samu zaman lafiya a basa ba.

“dole ne mu matasa mu riba duba abubuwan da Malamai ke ce mana, kuma mu riba yiwa juna adalci domin samun zaman lafiya” inji Dalon.

Muhammad Sani, daya daga cikin matasan da suka shirya taron ya ce sakamakon yadda ‘yan siyasa kanyi amfani da matasa wajan kawo rudu musamman da sunan addini yasa su shirya taron na ganin an samu kusantar juna domin kaucewa matsalar.

Ya ci gaba da cewa bana shekaru hudu kenan da suke shirya taron Maulidin Annabi Isa (as), a jihar da suke gayyatar matasan musulmi da bangarorin kiristoci domin tabbatar da ganin an samu hadinkai da fahimtar muna tsakaninsu.

“shekaru hudu kenan da muke shirya taro a irin wannan lokaci na maulidin Annabi Isa (as), muna gayyatar matasan musulmi da kirista da nufin samun hadinkai da fahimtar juna tsakanin matasa, domin mu ‘yan siyasa ke amfani damu” inji Sani.

Jama’a da dama da sukayi jawabi a taron sun yaba da bobarin matasan na ganin sun shirya irin wannan taro mai muhimmanci a daidai wannan lokaci.

 

Advertisement
Click to comment

labarai