Ranar Shayarwa: NAWOJ Ta Raba Kayan Tallafi Ga Iyaye Mata A Bauchi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ranar Shayarwa: NAWOJ Ta Raba Kayan Tallafi Ga Iyaye Mata A Bauchi

Published

on


A jiya ne bungiyar mata ‘yan jarida ta basa (NAWOJ) reshen jihar Bauchi ta raba tallafin kayyakin wa iyaye mata a jihar Bauchi, hakan na daga cikin bikin ranar Shayarwa ta Duniya ce wacce bungiyar ta gudanar a jihar.

Daruruwan mata ne suka ci gajiyar tallafin bungiyar mata ‘yan jaridan.

Da take jawabi a wajen kaddamar da rabon kayyakin, shugaban bungiyar mata ‘yan jarida reshen jihar Bauchi, Mr. Bulak Afsa ta ce, kayyakin tallafin da suka rabar wa iyaye matan sun yi ne domin raya ranar shayarwa ta duniya.

Shugaban NAWOJ din ta bara da cewa, tallafin nasu na daga cikin yunburinsu na barfafan iyaye mata dangane da muhimmancin shayarwa da kuma ci gaba da bayar da kula mai kyau ga jariransu.

Ta kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga iyaye mata a kowani lokaci suke shayar da jariransu da nonon uwa zalla a maimakon shayar da su da ruwa zalla ko madara ko wani abun na daban.

Ta ce, shayar da jarirai da nonon uwa zalla daga lokacin haihuwarsu zuwa wata shida zai bara sanya jariri ya samu lafiya da kuzari tana mai kiran iyaye su rungumi wannan dabi’ar hanu biyu-biyu.

Bulak Afta ta kuma shaida wa matan cewar, uwa tana dauke da kashi 90 na ruwan da ake son jariri ya samu, don haka ne ta bayyana cewar uwa mai shayarwa ba ta da bubatar neman wani abu don baiwa jaririnta na daga ruwa, tana mai shaida cewar nonon da ke jikinta ya wadaceta ta wadatar da jaririnta, don haka ne ta kirayi iyaye mata su rungumi hakan gadan-gadan domin kyautata lafiyar ‘ya’yansu.

Da yake tasa jawabin, shugaban sashin dabile yaduwar cututtuka na hukumar lafiya a matakin farko na jihar Bauchi, Alhaji Usman  Muhammad Shehu, ya nusar da iyaye matan da suka samu fadakarwar da cewar su daurar domin sanar da iyaye matan da suke cikin gida muhimmancin rigakafi wa yara daga lokacin da aka haifesu zuwa wata tara, inda ya bayyana cewar ta hanyar rigakafin nan ne ake maganin kamuwa da cututtuka da daman gaske da ke lahani wa yara.

Ya barfafi jawabinsa kan muhimmancin rigakafi, ya hakikance kan cewar ta rigakafi ne kadai uwa za ta kyautata rayuwar jaririnta.

Ababen da bungiyar mata ‘yan jaridan ta rabar sun kunshi kayyakin jarirai, sabulai, da kuma kayyakin wanke dauda da sauran ababen amfani ga iyaye masu shayarwa.

Wasu daga cikin ‘iyaye matan da muka zanta da su, sun nuna gayar farin cikinsu a bisa tallafin da bungiyar mata ‘yan jaridan ta samar musu, suna masu shan damarar ci gaba da kyautata rayuwar jariransu a kowani lokaci domin dacewa da kyautata rayuwar jariran nasu.

Bungiyar mata ‘yan jarida NAWOJ dai ta saba gudanar da irin wannan gangamin fadakarwa da kuma bayar da tallafi, hakan na daga cikin shirye-shiryen bungiyar dukka da kasancewarsu mata amma suna taka gagarumar rawa wajen kyautata rayuwar al’umma musamman na marasa galihu.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai