Sambo Aliyu Ya Zama Sabon Magatakardar FCE Kangare — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sambo Aliyu Ya Zama Sabon Magatakardar FCE Kangare

Published

on


Kwalejin ilimi ta Adamu Tafawa Balewa da ke Kangere ta amince da nada Alhaji Sambo Aliyu a matsayin sabon Rijistara na kwalejin.

Hakan ya biyo bayan wani zama ne da hukumar gudanarwa na kwalejin ilimin, zaman wacce ta yi a watan Agustan nan, inda a barshen zaman majalisar zastarwar kwalejin ta amince da nadin hadi da miba masa aiki a matsayin magatakarda.

Mun samu sanarwar hakan ne daga Kakakin kwalejin Bala Baban Kawu a cikin sanarwarsa da ya raba wa ‘yan jarida a Bauchi, ya bara da cewa an duba cancanta da kuma dacewarsa gabanin a amince masa kan wannan kujerar.

Sanarwar ta bara da cewa; tabbatar wa Alhaji Sambo Aliyu wannan kujerar, ya fito ne daga cikin wata bayanin da mai rikon mubamin rijistara na kwaljein Hajiya Hadiza Usman Isah ta fitar; ta ce,  kwalejin ta kasance babu rijista ne tun a watan Agustan 2016 biyo bayan sauya wajen aiki da aka yi wa rijistan farko na kwaljein Alhaji Garba Aminu zuwa jami’ar Kashere da ke Gombe, inda kwalejin ta ci gaba da tafiya da rijistaran riko, inda a halin yanzu kuma aka tabbatar wa Aliyu Sambo da kujerar ta rijistara.

Sanarwar ta bara da cewa; sabon rijistan ya nemi wannan kujerar ne da shi da wasu mutane tara, inda a yayin gudanar da tambayoyin gwaji aka amince da zaban Aliyu Sambo daga cikin masu neman kujerar.

Sanarwar ta bara da cewa, wannan kujerar da ya samu zai shafe shekaru uku a matsayin rijistarar kwalejin ta Adamu Tafawa Balewa da ke Kangere.

Baban Kawu ya bayyana ta cikin sanarwar cewar, gabanin nadin Sambo Aliyu a matsayin sabon rijistan, yana rike ne da kujerar mataimakin Rijista a kwajelin kimiyya ta Tatari Ali da ke Bauchi, baya ga nan, ya kuma rike mubamai daban-daban da suka hada da babban sakatare a gwamnatin Isa Yuguda da kuma kasancewa rijistara na ATAP amma na rikon kwarya.

Sanarwar ta bara da cewa, an haifi Sambe a baramar hukumar Jama’are da ke Bauchi, ya fara karatun Firamare dinsa ne a Zongo Kante da ke Jama’are daga 1971-1978, ya kuma halarci Sakandarin gwamnati da ke Gamawa a tsakanin 1971 zuwa 1983; sannan ya halarci kwalejin BACAS daga 1983-1985 daga nan kuma ya tafi jami’ar Bayero da ke Kano a 1985 zuwa 1988.

Sanarwar kwalejin ta hanun mai magana da yawunta, Bala Baban Kawu ta ci gaba da bayyana tarihin sabon magatakardarsu, ya ce, Sambo Aliyu ya fara aiki ne a kwajelin ilimi ta Azare a matsayin jami’in a sashin gudanar da mulki, daga bisani ya nemi sauyin wajen aiki ya koma kwalejin ATAP a matsayin mai tallafa wa rijistara, har-ila-yau Aliyu ya kasance sakataren dindindin a hukumar kula da ma’aikatan, ya kuma yi aiki a hukumar ‘yan fansho na bananan hukomi, ya kuma yi aiki a ma’aikatar da ke kula da tallafin karatu wa dalibai, sannan kuma ya yi aiki a ma’aikatar albarkatun ruwa na jihar Bauchi, yana da mata biyu da ‘ya’ya sha uku kamar da dai sauran kujerun da ya rike yadda sanarwar ta ce.

Yanzu haka dai ya amshi aiki a matsayin sabon rijsitaran kwajelin ilimi ta Kangere.

Advertisement
Click to comment

labarai