SDP Ta Yi Sabbin Shugabanni A Jigawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

SDP Ta Yi Sabbin Shugabanni A Jigawa

Published

on


Jam’iyyar SDP ta gudanar da zabeen sabbin ‎shuwagabanninta wadda zasu jagoranceta a kakar zabe mai zuwa ta 2019.

Jagoran jam’iyyar kuma dan takarar gwamnan jihar Alhaji Bashir Adamu Jumbo ya bayyana budurin jam’iyyar na kifar da gwamnati mai ci tareda maye gurbinta da ‘ya’yan jam’iyyar ta SDP.

Dantakarar gwamnan ya kuma sha alwashin inganta jindadin ma’aikata,mata‎, yara da matasa matubar suka bashi damar darewa kan karagar mulkin jihar.

Shi kuwa da yake nasa jawabin a jim-kadan bayan saba laya a matsayin shugaban jam’iyyar SDP a jihar Jigawa, Alhaji Abba Anas ya yi albawarin hada kan ‘ya’yan jam’iyyar domin tinkarar zabe mai zuwa na 2019.

Cikin sabbin shugabannin da aka zaba akwai Alhaji Abba Anas a matsayin shugaba, Alhaji Yusif Tela mataimakin shugaba, Alhaji Auwal Muhd Babaldu sakatare, Hajiya Balaraba Abdullahi shugabar mata, Abba Yahaya shugaban matasa da kuma Alhaji Bello Gada a matsayin sakataren yada labarai na jam’iyyar ta SDP a matakin jiha.

Advertisement
Click to comment

labarai