Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Tipa Ta Murbushe Dan Achaba Da Diyarsa A Bauchi

Published

on

A ranar Asabar wata tifa a Jihar Bauchi ta murbushe wani dan acaba tare da diyarsa yayin da ita kuma matarsa ta samu mummunar rauni, wannan lamari dai ya faru ne sakamakon mugun gudun da direban tifar yake yi. Hadarin ya farune a mahadan Bakin Kura cikin garin Bauchi. Majiyarmu ta bayyana mana cewa hadarin ya faru ne da misalin barfe 5.30 na yamma, inda ya janyo hankalin mutane tare da barsu cikin tausayi.

Wata mata wanda abun ya faru a gaban ta, ta bawa direban tifa laifi saboda mummunan gudun da yake yi ba tare da lura da wannan dan a ciban ba. ta bara da cewa “sakamakon mummunar gudun da direban tifan yake yi lokacin da ya zo mahadan, mai makon ya rage gudu sanda ya iso mahadan domin ya bawa dan acibon da ya dauko yarinyasa da kuma matarsa  dama ya wuce sai ya murbushesu tare da bugun wani mai mashin. Dayan mai mashin din da ya buga ya samu mummunar rauni.

“farkon mai mashin din da ya buga, ya mutu nan take tare da diyarsa amma ita matansa ta samu mummunar rauni. Hadarin baiwa mutane tausayi saboda kan mutumin ya fita yana ta jujjuyawa a kan titi kuma bwabwalwarsa ta bullubo waje.”

Shugaban hukumar kiyaye hadururruka Mista Paul Gua ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bada lambar tifar kamar haka 810503 ADJ da kuma mashina biyu duk suna cikin hadarin. Gua wanda shi ne mataimakin shugaban kiyaye hadurra ya bara da cewa, mutane biyar ne hadarin ya rutsa da su inda ya tabbatar da mutuwar dan acaba tare da diyarsa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: