Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan sanda Sun Tsinci Gawar Yaro A Kango

Published

on

‘Yan sanda sun tsinci gawar wani yaro dan shekara hudu a kango cikin Jihar New Medico dake basar Amurka yayin da yara 11 wanda aka ceto suna cikin wani mawuyacin hali, inji ‘yan sanda. An kama mutane guda biyu ranar Juma’a sakamakon binciken da ya gudana a kan neman yaran, a cewar Sheriff na ofishin New Medico.

“Mun gano sauran yaran ne ranar zagayowar haihuwar Abdul na shekaru hudu,” Sheriff Jerry Hogrefe ya bayyana haka ne ranar Talata tare da shan alwashi zai sun zabolo wanda ya aikata wannan mummunan aikin.

Shekara daya da gudanar da bicike, sai gashi an samu wani mutum mai suna Siraj Wahhaj dan shekaru 39 da haihuwa da laifin garkuwa da Abdul-Ghani.

Maman yaron ta gaya wa ‘yan sanda cewa, danta yana fama da matsalar bwabwalwa, ya tafi wajen shabatawa tare da ubansa tun watan Disamba kuma bai dawo ba.

Tun ranar 2 ga watan Agusta, Sheriff Hogrefe ya bayyana binciken da cewa “an zagaye kangon da ‘yan ta’addan suke” yayin da aka samu Wahhaj tare da wani saurayi mai suna Lucas Morten inda nan ne maboyansu. A washagarin ranar, jami’an tsaro suka kewaye wajen inda suka sami bindiga biran AR-15 guda 5 tare da albarusai guda 30 sai kuma bananun bindiga guda 4, an kuma samu baramar bindiga daya a cikin aljihun Wahhaj.

Morten da kuma Wahhaj ina zargin su da laifin sace yaran. Akwai wadan su mata guda uku wanda ake tunani cewa su iyayan wadannan yaran ne, daya daga ciki ‘yar shekara 15 amma a halin yanzu ana binciken su a kan lamarin.

A farkon binciken ya nuna cewa Abdul ba a ganshi ba, amma da jami’an tsaro suka tuhumi wadanda ake zargi sosai ranar Juma’a da kuma Asabar sai suka tabbatar da cewa lalle yaron yana wajen.

“Mun yi amfani da wadan su dabaro wajen gano yaron a inda suka a jiye shi,” inji Hogrefe.

Mahaifiyar Abdul ta sanar wa jami’an tsaro cewa Siraj Wahhaj ya gudu da yaronta ne sakamakon asiri da yake da shi.

Sauran yaran “duk an same su cikin boshin lafiya” inji Henry Barela lokacin da yake wa sashin kula da yara na New Mediko bayani.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: