Za A Bara Kudin Wuta Lantarki Da Kashi 14--Disco — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Za A Bara Kudin Wuta Lantarki Da Kashi 14–Disco

Published

on


Wani sabon tsari da gwamnatin tarayya ta bullo da shi kan masu amfani da wutar lantaki zai haifar da barin kudin da ake biya na amfani da wutar  na kashi 14 daga cikin kashi 100, wanda magidanta za su dinga biya a matsayin haraji a dukkan fadin basar nan. A cikin watan Yulin da ya gabata ne ministan wutar lantarki da ayyuka da gidaje Babatunde Fashola, ya bayyana cewa gwamnatin ta yi wannan barin ne ga masu amfani da wutar lantarkin domin su samu bayar da wutar kamar yadda ya kamata. Kuma kamar yadda ya ce dokar kamfanin wutar lantarkin sashi na 27  ta bayar da damar irin wannan barin.

Ya kuma yi bayanin cewa, tsarin zai tamaka wajen samar da wuta mai yawa musamman ga wadanda ke amfani da wutar mai yawa domin samarwa da mashinansu wutar lantarkin da za su yi amfani da ita.

Fashola, ya ci gaba da bayyana cewa, wannan sabon tsarin harajin zai taimaka wa kamfanonin rarraba wutar lantaki samun damar raba wutar kamar yadda ya kamata.

Sai dai a cikin wani bayanai da sashin wutar lantarkin ya fitar a kan wannan sabon tsarin na barin kudin harajin wanda aka raba wa manema labarai ya nuna cewa, wannan barin bai shafi gwamnatin tarayya ba. Bari ne kawai da ya tsaya a kan masu amfani da wutar a gidajensu.

Masu amfani da wuta a gidaje su ne ma fi rinjaye daga cikin masu amfani da wuta a dukkan fadin basar nan.

Saboda haka cire masu amfani da wutar a gidajensu daga cikin tsarin samun wani saubi na musamman ba zai haifarwa da kamfanonin rarraba wutar lantarkin da mai ido ba wanda shi ne biyasin da aka yin a cewa za su dinga bayar da harajin kashi 14 daga cikin kashi 100.”

Sai dai Disco, ya bayyana cewa, duk da cewa mun amince cewa, doka ta ba ministan dama yin barin kudin wutar, amma ba shi da ikon karbar barin kudin da muka samu ya yi amfani da su”

Kamfanonin samar da wutar lantarkin baruwar kudin da suke amfani da shi wajen sarrafa makamashin da kamfanin ke amfani da shi ne ya haifar da baruwar harajin, wanda idan ba haka aka yi ba zai jefa kamfanonin cin tsaka-mai-wuya.

“Ya ce, a halin yanzu ya kamata a caji masu amfani da wutar Naira 40/kwh. Amma  sai gas hi ana cazarsu Naira 26/kwh. Saboda haka akwai gibi Naira 14 wanda ya kamata a cike ta hanyar dora wa masu amfani da wutar a gigajensu.

Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun nuna, ya kamata gwamnati ta bayar da dama ga wasu kamfanonin da za su shiga harkar rarraba wutar, yadda za a samu watarsu wanda kuma hakan zai sa a samu gasa a tsakanin kamfanonin da zai sa ‘yan basa su more wa wutar lantarkin kamar yadda ya kamata.

“Saboda haka babbar hanyar da za a bi wajen samar da wutar lantarkin shi ne, shi ne a sa ido ga kamfanonin rarraba wutar lantarkin yadda za a tabbatar da cewa, al’umma na morar kudinsu, kamar yadda ya kamata.

Shi ma da yake nasa jawabin babban daraktan Cibiyar kasuwanci da masana’antu na jihar Legas Muda Yusuf, ya bayyana cewa, harkar samar da wutar lantarki har ka ce da ta zama ta kasuwanci  wadda ake bubatar samun riba a ciknta. saboda haka ya zama dole a ci gaba da laluben hanyar da za su samu ribar kuma a lokaci guda a samar da wutar da jama’a za su yi farin ciki da ita.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!