Hatsarin Mota Ta Ci Rayuwar Mutum 6 A Ribas — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Hatsarin Mota Ta Ci Rayuwar Mutum 6 A Ribas

Published

on


A kalla mutum shida ne suka mutu a yayin da wasu da dama suka gamu da munanan raunuka a wani hatsarin mota da ta auku a jiya a jihar Ribas.

Harin motar, wacce ta faru a tsakanin motoci biyu wnada suka yi taho mu kara a tsakaninsu, ta auku ne a daidai hanyar gabas maso yammacin karamar hukumar Emohua da ke cikin jihar ta Ribas.

Shaidun gani da ido; sun shaida cewar motar kasu Hiace dauke da fasinjoji 14 daga cikin jihar, wadanda suka nufi jihar Port Harcourt inda ta kara da wata motar dako a wannan hanyar.

Suka kara da cewa; wadanda suka gamu da raunuka an harzarta kaisu asibiti mafi kusa domin ceto rayuwarsu, inda matafiya ‘yan uwansu suka yi wannan jigilar.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, Nnamdi Omoni ya ce ba zai iya tabbatar wa ‘yan jarida da wannan lamarin ba a lokacin da suka tuntubeshi, inda ya nunar da cewar daga baya zai iya samar da cikakken bahasi

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!