Abubakar Isma'ila Isa Da Siyasar Katsinawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Abubakar Isma’ila Isa Da Siyasar Katsinawa

Published

on


Malam Abubakar Ismaila Isa, CNA mni, da ne ga Alhaji Samaila Isa Funtuwa, don haka ba ya bukatar gabatarwa a al’ummar Nijeriya ba ma jihar Katsina kadai ba.

Dadin dadawa Malam Abubakar ya nemi yin takarar Gwamna a karkashin jma’iyyar CPC a shekarar 2011, haka kuma a shekarar 2015 ya nemi yi wa jam’iyyar APC takarar Gwamna. Wato bayan an yi hadaka tsakanin jma’iyyun CPC, ANPP da kuma jam’iyyar ACN, in da aka koma APC.

A wancan karon Allah bai nufa Malam Abubakar Ismaila Isa ya sami nasara ba a zaben fid da gwani da aka yi ba. Amma duk da haka bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da gudunmawa don ciyar da jam’iyyar APC da jihar Katsina ba.

Malam Abubakar Ismaila Isa na da kudurori da daman gaske don ganin ya fidda Katsinawa daga cikin halin da suke ciki na rashin isassun kayan more rayuwa da suka zama abin bege ga al’ummar jihar. Domin shi a kullum talakan jihar Katsina ne a gabansa.

Katsinawa na shaukin ganin rayuwarsu ta inganta musamman a irin wannan lokaci da suka yi sa’ar ganin cewa shugaban talakawa, Muhammadu Buhari ne shugaban kasa kuma dan asalin jihar ne. Ba zai yarda ta batun nada Kantomomi ba ko kuma nada ma’aikatan Gwamnati a matsayin wadanda za su rike Kananan Hukumomi ba. Wato zai bi tsarin mulki Nijeriya sau da kafa.

Idan Abubakar Ismaila Isa ya sami goyon bayan al’ummar jihar Katsina har ya kai ga zama Gwamnan jihar yana da kudurori da suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye ta dukkan bangarorin rayuwa da kuma zamantakewarsu.

Daga cikin kudurorin, Malam Abubakar Ismaila zai tabbatar ya ci gaba da yin zaben Kananan Hukumomi a jihar. Don haka ne zai rage matsanancin talauci da ake fama da shi a jihar.

Zai dawo da biyan kudin jarabawar kammala karatun sakadare ta WEAC da NECO ga ‘yan jihar, wanda wannan gwamnati ta janye biya musu. Hakan zai taimaka wajen ragewa iyayen da ba su da karfin biyan kudin wahalhalun da suke fada da su. Sannan zai ci gaba da biya wa daliban jihar kudaden yin karatu a kasashen waje.

Malam Abubakar zai tabbatar an dauki ma’aikatan da ke aikin wucin gadi aikin dindindin. Domin hakan ne hanya daya da za a saka wa irin wadannan mutane da suka dade sun aiki ba tare da an daukesu aikin a matsayin ma’aikata ba.

Samar da tsari mai kyau da zai kula da tallafin takin zamani da sauran allafin aikin gona. Haka kuma zai tabbatar takin zamani ya isa hannun manoma a kan lokaci ba sai damina ta kare ba.

Zai kuma ci gaba da samar da tallafi ga masu fama da cututtuka a asibitoti. Musamman cututtukan da suke da illa ga yara kanana. Haka kuma zai gina asibitoci tare da samar da kayan aiki ingantattu don kula da lafiyar al’umma. Suma ma’ikatan kula da lafiyar tun daga Likitoci da sauran ma’aikata dole za a dauki kari, sannan kuma a rinka horar da su kodayaushe don ganin sun kula da mutane yadda ya kamata.

Haka zalika, Malam Abubakar zai yi duk abin da ya kamata don ganin an nemo masu zuba jari daga ciki da kuma kasashen waje don zuba jari a jihar ta fuskar noma da kiwo da kuma masana’antu da sauransu.

Suna Malaman makarantun jihar za a samar tsarin horar da su ta hanyar hada hannu da kungiyoyinmu na Malamai da kuma turasu makarantu don karo ilimi.

Daya daga cikin masu fafutukar ganin Malam Abubakar Ismaila Isa ya zama Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Nura Dan Mummuni, ya bayyana cewa suna da kudurorin ganin sun yi abin da wata gwamnati ba ta taba yi ba a Katsina.

Ya ce dan takararsu Matashi ne mai jini a jika. Saboda haka ya yi kira ga al’ummar jihar da su goya musu baya ta hanyar zaben Malam Abubakar Ismaila Isa a matsayin Gwamnan jihar Katsina a shekarar 2019 don inganta rayuwar al’umma.

Malam Nura Dan Mummuni ya ci gaba da cewa sun jaraba dattawa da dama a wannan kujera ta Gwamna a jihar sun ga kamun ludayinsu. Don haka ya ce lokaci ya yi da ya kamata a zabi matashi don suma a ga irin na su kamun ludayin.

 

Advertisement
Click to comment

labarai