An Bukaci A Kara Zuba Jari A Tashoshin Jiragen Ruwa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

An Bukaci A Kara Zuba Jari A Tashoshin Jiragen Ruwa

Published

on


Don magance cinkosun kayan da ake saukewa a tashar Apapa dake cikin jahar Legas, masu ruwa da tsaki sun bayar da shawara ga gwamnati data baiwa masu zuba jari kwarin gwaiwa don a giggina wasu tashoshin na ruwa. Masu ruwa da tsakin sun bayyana hakan ne a taron da aka yi akan kayan cikin gida a jahar legas, inda suka yi nuni da cewar akwai manyan kalubale da dama da tashshin suke fuskanta. Da yake gabatar da jawabinsa Mista Andy Isichei, ya yi nuni da cewar, wasu tashoshin ba’a kula dasu yadda ya kamata. Ya yi nuni da cewar, akwai bukatar a baiwa masu zuba jari kwarin gwaiwa akan fannin tashoshin jaragen ruwa, musamman don samar da kayan aiki. Acewar sa, dalilinda ya sanya babu tanuna da yawa a jahar Legas shine, tashoshin dake a kudu basu da hanyoyi masu kyau.

Shi ma wani mai ruwa da tsaki kuma sakataren kungiyar masu sufruri na kasa Godwin Ikeji, a hirar da ya yi da manema labarai a wurin taron ya baiwa gwamnati shawara data dinga baiwa masu zuba jari kwarin gwaiwa don kwashie kwantanonin da ake jibgewa mai makon jigilar su ta hanya, inda ya yi nuni da cewar, mafiyawanci suna tare hanyoyin dake gefen na Apapa.

Da yake mayar da martani Mataimakin Janar Manaja na sashen tsara bayanai ta hukumar Mista Isah Suwaid, ya sanar da cewar tuni hukumar ta kafa kwamiti da zai yi dubi akan matsalar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai