Isah Wakili Ya Amince Da Takarar Majalisar Wakilai Ta Kasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Isah Wakili Ya Amince Da Takarar Majalisar Wakilai Ta Kasa

Published

on


An nemi ‘yan takarkarun siyasa da su hada kai su ciyar da kasa da jam’iyyar APC gaba, mataimakin ma’ajin jiha na jam’iyyar APC a jihar Neja, Malam Audu Ibrahim (Abiola) ne ya yi kiran a lokacin da dan takarar kujerar majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar Bosso /Paiko, Hon. Isah Wakili ya ziyarci shugabanni jam’iyyar da dattijai a sakatariyar karamar hukumar da ke Bosso.
Malam Audu ya ce akwai ‘yan takara da yawa a jam’iyyar nan amma mutum daya ne Allah zai baiwa shugabancin a cikinsu, dan haka su sani siyasar da za a yi yanzu siyasa ce ta kai da halin ka, duk dan takarar da ya tsaya zaben fidda gwani kuma bai kai ga nasara da ya hada kai da wanda ya samu nasara dan ganin an samar da wakilci mai inganci.
Lallai a wannan tafiyar akwai gyara, domin an zabi mutane an tura su majalisa sun tafi dan wakiltar kansu ba jama’ar da suka kai su ba, dan haka a wannan karon duk mai tunanin zai yi kamun kafa da wani jigon siyasa ya tabka kuskure ya zama wajibi su koma su nemi amincewar jama’a.
Ya zama wajibi ga talakawan kasar nan ga duk mai son cigaban kasa da jam’iyyar APC da kuma amincewa da kudurorin shugaba Muhammadu Buhari da ya tabbatar ya mallaki katin zabe dan da shi ne kawai za ka iya nunawa Muhammadu Buhari soyayya ta gaskiya da zaben jama’a nagartatu da zasu taimaka ma shi a majalisar kasa.
Da yake bayani ga shugabannin jam’iyya da dattijai, Hon. Isah Wakili ya ce ya ziyarci sakatariyar ne dan nan ne asalin gidansa, dan haka a matsayin shi na dan siyasa mai kishin kasa yazo ya fara gabatar da kanshi ga shugabanni da iyayen jam’iyya. ” Maganar takarar majalisar wakilai ba wai ina da burin hakan domin kamar yadda aka tsara mu mutanen Bosso ke da alhakin fitar da dan takara tunda Paiko ta kammala wa’adin ta biyu na wannan kujerar”.
Shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Bosso wanda ya samu wakilcin mataimakin sa, Malam Ibrahim Makeri, ya ce Hon. Isah Wakili ne dan takarar majalisar na farko da ya nuna muradinsa wanda har ya kai ga ziyarar sakatariyar jam’iyyar dan nuna bukatar sa. Saboda haka mu a ham’iyyance mun amince da goyon bayan jam’iyya akan wannan takarar.
Jam’iyyar ta sha alwashin ba za ta sake marawa ma wani dan takarar da bai san aikin da aka tura shi dan wakiltar jama’a ba, ya kamata ‘yan siyasa su rika tafiya suna duba baya dan ba su ne suka kai kansu a wannan wajen ba.
Rashin mai da hankalin zababbun ‘yan siyasa yasa da daman su basu san halin da yankunan su ke ciki ba, amma da mutum jama’a yake wakilta da ya zama gwarzo a fagen al’umma, amma dai a wannan tafiyar halin ka ne zai baka dama.

Advertisement
Click to comment

labarai