Kudaden Kaddararorin Fansho Ya Haura Naira Tiriliyan 8.23 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Kudaden Kaddararorin Fansho Ya Haura Naira Tiriliyan 8.23

Published

on


A bisa bayanan da aka samu daga hukumar fansho ta kasa NPC, bayanan sun nuna cewa, kimanin kadarori a karkashin shirin biyan kudin fasho, sun haura zuwa Naira Tiriliyan 8.23 a karshen tsakaiyar shekarar  2018. Addain ya nuna cewar, kudaden da aka zuba, sun karu daga  miliyan 312,291 7.89 a cikin watan Disambar 2017 zuwa Naira Miliyan  8.14 a cikin watan Yunin 2018. Hukumar ta kara da cewa, kadarorin da aka kiyasta da aka zuba na fanshon sun kai Naira tiriliyan 8.23 a cikin watan Yunin 2018. Wannan yana nuna cewar, an samu kari na Naira Biliyan 716.94 daga yawan Naira tiriliyan 7.52 a a ranar talatin da daya na watan Disambar 2017. An kuma danganta samun wannan karin a bisa shigo da sabon zuba kadi da kuma jarin da aka zuba. A cewar hukumar, masu hada-hada a fanin sun zuba jarin  isassun kudade a cikin shirin. Rahoton na hukumar ya kara da cewa, wasu daga cikin kudaden an zuba jarin ne a hukumomin da takardun kasuwanci da kudaden kasahen waje da sauransu. Sauran zuba jarin sun hadada na kudaden gidaje dana sauaran kayayyaki da kuma sauran kadarori. Hukumar ta kara da cewa, don a habaka biyan fanshon duk wata, aka kirrkiro da shirin. Bugu da kari, hukumar ta ce, kudaden da aka tara a karkashin shirin na PFA, a kan sauran na RSA, mafi yawancin ‘yan fansho zasu yi amfani da kudaden wajen haka fanshon da suke karba duk wata. Har ila yau, hukumar zata bukaci amincewar sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustpha a kan kaddamar da kara habaka fanshon wanda ha kan ya janyo aka samun karin fanshon na wata-wata a cikin tsarin karkashin cire kudi.Tuni dai a karkashin shirin na PFA aka fara biyan fasnhon na ‘yan fansho wanda zai fara aiki a watan Disambar 2017. Kuma kaddamar shirin na fanshon, yana daya daga cikin na farko da hukumar ta ci nasara a kai tun lokacin da aka fara aiwatar da shi.

A cewar hukumar, ta samar da matakai na cikin gida da zasu yi aiki sosai a kan abin da ‘yan fanbshoin suke samu kuma tasha alwashin ci gaba da aiwatar da shirin a bisa yadda doka ta tanada.

Advertisement
Click to comment

labarai