Makarantar El-buhaj "Royal Academy" Ta Yi Bikin Yaye Dalibanta. — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Makarantar El-buhaj “Royal Academy” Ta Yi Bikin Yaye Dalibanta.

Published

on


An bukaci Gwamnatin Kano ta rika tallafa wa masu makarantu masu zaman-kansu da bashin kudi mai saukin biya domin ci gaba da bada gudummuwarsu wajen samarda ilimi a tsakanin al’umma a jahar Kano. Daraktan makarantar El-Buhaj Academy, Alhaji Abubakar Abdullahi ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a wajen bukin saukar karau da raba kyautuka ga hazikan dalibai karo na uku da makarantar ta gudanar ranar Asabar a dakin taro na Mambayya.

Ya kara da cewa yakamata Gwamnatin ta Kano ta yi koyi da  Gwamnatocin  Anambura da Imo da suke baiwa  masu makarantu masu zaman-kansu  bashi  saboda sun fahimci  harkar ilimi abune da take bukatar a bata kulawa ,in aka sami irin haka a Kano zasusan ana yabawa da irin gudummuwarada suke bayarwa.

Alhajji Abubakar Abdullahi ya yi nuni da cewa ya kafa makarantar El-Buhaj Akadami ne a shekarar 2011 bayan ya bara aikin Banki saboda sha’awarsa da koyarwa tun yana dan karamin Yaro.Ya soma makarantarne da dalibai 35 wanda a yanzu makarantar tanada dalibai 365 da suke daukar darasi a fannoni da dama.

Yace makarantar tanada fannin Islamiyya da ake koyarda Tahfiz wanda a barama yara da dama sun sauke da haddace Kur’ani a bana ma akwai dalibai 10 da suka sauke.Makarantar an doratane akan tarbiantarda Yara da basu Ilimi mai inganci da kuma jagoranci domin su zama manyan gobe nagari da zasu taimakawa al’umma.

Daraktan  na makarantar E-l Buhaj Royal Akadami yace makarantar tanada kyakkyawar alaka da fahimtar juna tsakaninta da iyayen yara  suna kuma daukar nauyin Yara marayu dalibai da iyayensu suka rasu har zuwa matakin jami’a yanzu haka ma akawai dalibai marayu uku da suke cikin tsarin.

Yace babban kalubalenda suke fuskanta shine na yawan karbar haraji da Gwamnati take daga garesu ta bangarori da dama da sukeso a sassauta musu akai la’akari da irin tallafinda sukewa Gwamnati wajen rage mata nauyin ilmantarda al’umma.

Yace makarantar tasu tana koyarda wani sashe na dalibanta ne da suke ajin daya zuwa uku da tsari na koyarwa da karamar Kwamfuta da ake cewa tablet da suka samo dan amfanin malaman makarantar da kuma dalibansu nan gaba kadan suma wadanda suke kananan ajujuwa  za’a dorasu akan tsarin domin tafiya daidai da zamani.

Alhaji Abubakar yace dalbanda sukayi saka a makarantar a bana sun hada da wanda suka kamala manyan ajujuwa na sakandire 12 da wanda zasu tsallaka babban aji 17 da kuma yan ajin reno da zasu furamare guda 45.

Shima a nasa bangaren Shugaban Iyaye da malamai na Makarantar Alhaji Balarabe Yaro  ya nuna cewa makarantar tana amfanarda ya’yansu wajen basu ilimi mai nagarta da suka tabbatar kudinda suke biya yana amfanar yaran.

Yace sun gamsu matuka da tarbiya da karatunda yaran ke samu  a bangaeren Boko dana Kur’ani wanda akan haka suka kawosu.

Alhaji Balarabe Yaro irin wadannan makarantu masu zaman kansu suna taimakawa  wajen bunkasa ilimi  yace Yaransa da suke karatu a makarantar 13 suna samun kulawa.Yayi kira ga iyaye su rika biyan kudin makarantar ya’yansu akan lokaci dabin ka’idar makarantar.

Advertisement
Click to comment

labarai