PenCom Ta Fara Biyan Kashi 25 Na Kudin Wadanda Suka Yi Ritaya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

PenCom Ta Fara Biyan Kashi 25 Na Kudin Wadanda Suka Yi Ritaya

Published

on


Hukumar Fansho ta kasa ta sanar da cewar,  soke biyan kashi ashirin bisa dari na biyan ‘yan fansho a karkashin shirinta na biyan fansho,inda kuma ta bayar da umarnin da’a dawo da ske biyan na kashi ashirn da biyar da ake ada. Darakta Janar ta hukumar mai rikon kwarya Uwargida Aisha Dahir-Umar,ce ta sanar da ha kan a a ranar Alhamis data gabata a taron inshora da aka gudanar a a ranar Alhamis a jihar Legas. Aisha wadda shugaban sashen zuba dashe na hukuamar ya wakilce ta a wurin taron Olulana Loyimi ta ci gaba da cewa, hukumar ta yanke shawawar sokewar ne sabotda sukar da akaita yi a kan batarwar. Ta ce, Kamar yadda kuka sani ne, an dakatar ne a ranar sha biyar ga watan Mayun 2018 kuma masu ruwa da tsaki suma sun nuna damuwar su a kan ha kan kuma hukumar ta umarci masu gudanar da biyan fanshon dasu aiwatar da sabon tsarin na biyan. Acewar ta, hukumar a cikin watan Mayu ta fitar da tsarin na PFAs don a rabar da takardun biyan kudin gay an fanshon, inda ya kai kashi sha shida bisa dari. Ta bayyana cewar ‘yan fanshon suna nuna rashin jin dadin su a kan kasa samun kashi ashirin da biyar din bisa dari a cikin tsarin na RSAs da dokar ta bayar da dama. Sashi na uku daya a cikin baka na dokar jihohi ta shekarar 2014 ta bayar da damar biyan fansho ga wadanda suka kai shekara hamsin a kan tsarin RSA. Yadda ake auna takadar da ake rabarwa ta fansho a wata wadda ke kunshe da ranar ranar haihuwa da albashi na karshe kafin yin ritaya.

Advertisement
Click to comment

labarai