Sarakunan Fulani Sun Koka Kan Aikin Hukumar Zabe — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Sarakunan Fulani Sun Koka Kan Aikin Hukumar Zabe

Published

on


Shugaban kungiyoyin makiyaya da sarakunan fulani sun koka kan yadda aka mayar da al’ummominsu baya wajen basu dama kamar kowanne dan kasa na hakkin kada kuri’a yadda ya kamata a lokuttan zabuka a kasar nan. Domin tun da aka bude fagen bada kadin zabe ga wadanda shekarun su yakai da wadanda suka canja mazaunai ba wani tanadi da hukumar tayi na sanar daruruwan makiyaya da ke zaune a cikin dazuka illa kawai suna jin labaran cewar ana gab da rufe shirin a cikin wannan watan da ake ciki.

Ardo Bello Ahmed Garatu, ko’odineta na kasa na kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association Of Nigeria kuma sarkin fulani Garatu da ke karamar hukumar Bosso, ya ce su kan hukumar zabe ta mayar da su baya domin ba a taba tuntubarsu ba ko sanar da su wani aiki na hukumar a matsayin su na ‘yan kasa kamar yadda ake wa sauran kungiyoyi da sarakunan al’umma ba.

Ya ce misali a kasar Garatu sun bukaci a bude mazaba ta yadda daruruwan makiyaya zasu samu damar jefa kuri’a a lokuttan zabe kamar yadda ya kamata, domin idan ka duba a nan Garatu kawai muna da cibiyar koyar da ‘yayan makiyaya wadda ake cewa Bello Garatu Nomadic School kusan nan ne matattaran makiyaya a yankin mun bukaci a bude mazaba a nan ta yadda kowanne bafillani zai iya zuwa ya yankin katin zabe ko jefa kuri’a don ta nan ne kawai muke ganin hukumar zabe za ta bamu damar yin zabe tunda duk al’ummar fulani zalla a wajen amma har zuwa yanzu shiru kamar an shima dussa, wanda mu muna kallon ana nuna mana bambanci.

Ardon ya ce in ban da ku ‘yan jarida ba mu san da maganar bada katin zaben nan ba balle mu sanar da jama’ar da muke jagoranta muhimmancin sa ba sai kawai yau da ku ka zo da maganar shirin rufe aikin, to wanda bai san ana yi ba, ina kuma zai fara tunda an ce za a rufe ne. Muna da dubban jama’a a nan kuma sun is a jefa kuri’a ba su da katin zabe, muna wadanda ba sa gida koda aka yi wancan na baya kuma suna bukatar mallakar katin yanzu ganin halin da ake ciki na waye wa da kuma bukatar jefa kuri’a.

Ba nan Garatu ba ko jama’ar Zukogi da ke Kodo a yankin Beji na fuskantar irin wannan matsala, ka ga ke nan dubban makiyaya ne ba zasu samu damar jefa kuri’a a wannan zaben mai zuwa.

Ina baiwa hukumar zabe ta kasa shawara dan kaucewa cigaba da tauye hakkin makiyaya shawarar idan irin haka ya taso a rika tuntubar sarakunan makiyaya da kungiyoyin su ta haka ne sakwanni zai rika isa ga wadanda suke zaune a cikin dazuka suna kiwo, fulani mutane ne masu biyayya, masu bin dokokin kasa bai kamata idan irin ya taso ba a rika mayar da su baya ba, dan ina da tabbacin ba nan yankin kawai muke da irin wadannan matsalolin ba, ba a tuntubar abu sai lokaci ya kure.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta jihar Neja, sarkin fulanin Lapai, Ardo Abubakar Salihu Dikko Sha Kallo kuma tsohon shugaban matasa na jiha na kungiyar, ya ce idan har hukumar zabe da gaske ta ke ya kamata ta tuntubi kungiyoyin makiyaya domin su ne kadai suka san inda makiyaya ke zaune, sune kadai zasu iya wayar da kan makiyaya domin sun san al’adu da yadda zasu iya kai sakwanni ga makiyaya.

Ya ce samar da mazaba a inda ya dace ne kawai zai baiwa fulani damar marawa hukumar baya, domin bafillatani ba zai bar daji ya dawo gari ya zauna dan jiran abinda hukumar zabe za tayi ba tunda dai bai sani ba, amma ofisoshin sarakunan gargajiya da na kungiyoyin makiyaya na nan cikin gari, a kowanne lokaci nan ya kamata a rika tuntuba su kuma sai su tara jama’a su sanar da su.

Ko yanzu hukumar zabe ta shirya, in har ta neme mu da mu tara jama’a kasa da awoyi zasu sha mamaki, amma a gaskiya akwai alamar tambaya ga ita hukumar zabe kan mu makiyaya, shi ba wani lauje a cikin nadi kuwa.

Tunda farko shugaban hukumar zabe na kasa, mai kula da jihar Neja, Farfesa Samuel Egwu, shi ne shugaban hukumar na farko wanda ya fara ziyartar sakatariyoyin jam’iyyun siyasa tun bayan kama aikinsu a hukumar dan tabbatar jam’iyyun na tafiyar da ayyukan jam’iyya kamar yadda ya kamata. A lokacin ziyarar ya baiwa jam’iyyun siyasa damar yin tambayoyin game da aikin hukumar da neman shawarwarin su ta yadda za a cigaba.

Da yake karin haske ga manema labarai, Farfesa Samuel Egwu a ta bakin jami’in yada labaran hukumar, Malam Ibrahim Abari, ya ce hukumar za ta rufe cigaba da bada katin zaben ranar 17 ga watan Augustan nan da muke ciki. Kuma gwargwadon hali kamar yadda doka ta basu damar sun sanar lokacin da a bude cigaba da fara aiki kuma yanzu sun sanar dan rufe wa kamar yadda doka ta ba su dama.

Ya ce hukumar ta fara aikin bada katin zaben tun watan Afrilun 2017, daga Afrikun 2017 zuwa watan Disamba ta yi rajistan mutane 93,0208 kuma adadin mutane 82,896 sun karbi katinunan kuri’unsu. Kuma ko bayan cigaba da aikin a watan janairun 2018, mutane 198,038 ne aka yiwa rajistan wanda hakan na nuna cewar adadin mutanen da suka fito sun dara na shekarar bara.

Ya ce ga mutanen da aka yiwa rajistan yanzu za su samu na su katin kafin zaben 2019 mai zuwa, tun cikin Yunin wannan shekarar muka fara yekuwar cigaba da aikin nan da sanar da jama’ar cewar wadanda ba su karbi katin su ba su ziyarci cibiyoyin mu dan karban katin su, misali na ce maku a 2017 bugo rajistan 82,896 cikin 93,0208 da aka yiwa rajistan amma 26,673 ne kawai suka karbi katin ke nan hakan na nuna kashi 32% ne kawai suka karbi katin baya a bugo su.

Mun yi wa 6,673 da rajistan kan canja wajen zama a 2017 din zuwa yanzu cikin dubu shida da doriyar 61 kawai suka karbi katin wanda in ka duba 1% ne kawai suka karbi na su, duk sauran katunan  kuri’un suna nan hannun mu.

Saboda haka maganar korafi bai taso ba hukumar zabe na bakin kokarinta akan wannan aikin, abinda muke nema ga jama’a shi kowanne lokaci kofa a bude ta ke ga duk wanda ke da shawara  ko kuma korafi, ya kamata kungiyoyi masu zaman kansu da ‘yan siyasa da su taimaka mana a duk lokacin da su ka ji sanarwa daga gare su sanar da na kusa da su.

Advertisement
Click to comment

labarai