Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda Jihar Gombe Sun Cafke Barayi 116

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe sun ce, sun kama mutane guda 116 da suke zargi da laifuffuka da dama a cikin shekaran 2018. Kwamishinar ‘yan sandar Jihar  Mista Shina Olukolu shi ya bayyana hakan a ranar Asabar.

“Daga watan Janairu zuwa watan Yuli na shekara 2018, rudunarmu ta kama mutane 116 dake zargi da laifuffuka da dama a cikin Jihar. A cikin mutane 99 wandan da ake zargi an kai su kotu kuma an same su da laifin da ake zarginsu da shi harma an daure su saura 17 suna jiran shari’a,” inji shi.

Kwamishinan ya ce, an amso makamai a wajen wadanda ake zargi.

“Mun amso bidiga  guda daya, karamar bindiga guda biyu, adduna guda 250, huka guda 255, kwari da gwafa guda 20, gatari guda 33 da kuma takobi guda uku.

“ Wadansu kayayyakin da muka amso sun hada mashina guda hudu tare da takardar mallan mashin na karaya, wayoyi guda shida, kwamfiyuta kiran Lenobo guda daya, caja guda biyu da kuma batirin da yake cajin waya guda daya,” inji shi.

Olukolu ya sha alwashin cewa, rundunar ‘yan sandar Jihar Gombe za ta dauki matakin dakile duk wani muyagun laifuffukan dake daddabar Jihar. Ya ci gaba da cewa, rundunar ta kaddamar da wadansu dabarun yakir manya laifuffuka ta yanyar saka idanu a kan cibiya sadarwa domin jiyadda rundumar muhanman bayanai a kan‘yan ta’addan cikin Jihar baki daya.

“Tare da saka idanu a kan cibiyar sadarwanmu, za mu iya samun bayanai wanda za su taimaka mana domin gane masu laifuffuka daban-daban a cikin fadin Jihar. Wannan shi zai taimaka wa rundumar wajen samun nasara. Ya jaddada cewa, nasarar da muka samu a shekarar 2018 ta ta’allaka ne bisa bayanin sirri da muka samu a tsakanin ‘yan sanda da wasu jami’an tsaro da kuma mutanan Jihar Gombe gaba daya.

Olukolu ya yi kira ga mutanan Jihar da su dunga taimaka wa ‘yan sanda da cikakkyan bayanai a kan ‘yan ta’addan, wannan shi zai bawa ‘yan sanda daman gudanar da aikinsu yadda ya kamata, inji shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: