Za Mu Dau Mataki Kan ’Yan Siyasar Da Ke Belin ’Yan Daba -Magaji Majiya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Za Mu Dau Mataki Kan ’Yan Siyasar Da Ke Belin ’Yan Daba -Magaji Majiya

Published

on


A cikin kokarin da ake na ganin an kawo karshen matsalar shaye shaye da kuma fatauncin miyagun kwayoyi wanda Kungiyar Ma hadu mu gyara ta shirya domin tunkarar wannan babbar Matsala, alokacin Taron Kakakin Hukumar ‘yan Sanda Na Jihar Kano SP Magaji Musa Majiya ya yi guda harda zamiya, musamman ganin yadda jama’a suka amsa kiran da Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Kano ke yi domin hada hannu da al’ummar unguwanni domin ganin ana kawo karshen wannan mummnar dabi’a.

Magaji Musa Majiya ya ci gaba da cewa Ko shakka babu Hukumar ‘yan Sanda na alfahari da wadannan Kungiyoyi da a halin yanzu ke tallafawa Hukumar ‘yan sanda ta fuskar yaki da miyagun laifuka, ya ce hada kan al’umma shi ne zai kara tabbatar da nasarar wannan aikai da aka sa gaba, musamman ganin yadda ‘yan Kwamitoci ke hada karfi tare  da iyayen kasa masu unguwanni da sauran masu kishin cigaban Jihar Kano. Saboda haka sai Kakakin Rundunar ‘yan Sandan na Kano Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa ‘yan Kwamiti su shakuruminsu suna da cikken goyon bayan mai girma Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano.

Hakazalika SP Magaji Musa Majiya ya bukaci ‘yan kwamiti da cewa suyi duk mai yiwu kar wani dan daba ya aikata ta’asa kuma abarshi ya agundu, sannan kuma ya yi albishir ga mahalarta taro musamman ‘yan Kwamiti cewa da yanzu sun shata layi daga wannan lokaci duk wani dan Siyasa da aka kama dan Daba yazo ya karbe shi sai sun fito ta kafafen yada labarai sun sanarwa jama’a cewa wane ne ya zo ya karbi dan daba wane saboda haka kar a zabeshi. Daganan sai ya bukaci ‘yan Kwamiti da cewa su guji daukar doka a hannu, duk idan suka hadu da wani ma’aikata laifi su damka shi a hannun ‘yan sanda kar su doke shi ko amfani da makami akansa.

Shi ma da yake gabatar da na sa Jawabin Kwamandan Hukumar dake yaki dasha tare da fataucin miyagun kwayoyi na Jihar Kano Malam Hamza Umar wanda Ibrahim Mamman ya wakilta ya bayyana cewa shirye shiryen hukumar na gani an kamo bakin zaren wannan bakar ta’ada ya yi nisa, ya ce akwai bukatar al’umma su kara hadu hannu da sauran Jami’an tsaro wajen kawar da shaye shaye da ke neman zamewa jama’a kadangaren Bakin tulu. Ya yi tsokaci kan yadda aka warware matsalolin wurare irin hauren joka, Island da sauransu, don haka ya bukaci iyayen kasa dasu ci gaba bayar da dukkna goyon bayan ga ire iren wadannan kungiyoyi. Ya ce muna yin wannan aiki ba dare ba rana wanda kwanan nan aka kashe mana wani ma’aikaci a bakin aiki, kuma hakan bai sa mun daga kafa ba. Haka kuma Ibrahim Mamman ya bayyana cewa ba inda ya kai Jihar Kano samun goyon bayan mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II kan yaki dasha tare da fataucin miygun kwayoyi.

Daya ke gabatar da Jawabinsa amadadin kungiyoyi masu zaman kanasu Khalifa Dokaji ya bayyana wasu da ga cikin abubuwan da ke zaman kadangaren bakin tulu a wannan bangare, ya ce maganar fataucin miyagun kwayoyi sanin kowa ne jami’an tsaro sun kwana da sanin masu wannan bakatar ta’ada, sannan kuma idan ma an kama mai laifi sai kaji ana ce wai ba’a samu wasu kwararan shaidu ba wanda za’a iya hukunta wanda aka kama, haka kuma aduk lokacin da aka gudanar da kamen masu aikata wannan laifuka cikin kankanen lokaci sai kaga sun fito.

Dokaji ya kuma koka kan makudan kudaden da Gwamnatoci ke warewa domin yakar wannan bakar  sana’a, ya kuma yi tsokanci kan makudan kudaden da gwamnatin Kano ta ware a shekara 2016, 2017 zuwa 2018 wanda yanzu haka aka ware Sama da Naira Miliyon 30, amma me wadanan kudede suka samar ta fuskar nasara. Ya kuma bayyana cewa a lokuta daban daban da yawa jami’an tsaro ake hada baki wajen fitar da duk wani dan gata da aka kama, aka koma kama ‘ya’yan marasa galihu, sannan kuma ya bayyana cewa rashin ayyukan yi na taimakawa kwarai da gaske.

Ana sa jawabin Malam Isma’il Yusif Makwarari wanda shi ne ya kirkiri wannan tsari wanda ahalin yanzu koko har ya zama masaki, ya bayyana cewa babban dalilin samar da wannan shiri shekara guda da rabi da fara wanan yunkuri, wanda ahalin yanzu al’umma sun fara fahimtar muhimmancin wannan kyakkyawan tunani, ya ce fatan mu shi ne sauran unguwanni ma suyi kokarin samar da irin wadannan kwamitoci domin hada karfi da karfe wajen yakar wannan bakar ta’ada. Makwarari ya ce akwai gudunmawar da wannan hadin kai tsakanin kafafen yada labarai da kuma masu unguwanni wanda ake fatan isar da wannan gagarumin sako ga al’umma. A karshe ya bukaci jami’an tsaro dasu ci gaba da baiwa kungiyoyin sa kai na unguwanni dukkan goyon bayan da ake bukata domin cin nasarar aikin. 

 

Advertisement
Click to comment

labarai