Connect with us

DAGA NA GABA

Mu Na Da Hujjojin Barin Jam’iyyar APC –Ibrahim Danbaba

Published

on

‘’’Mu ‘yan majalisar tarayya daga jihar Sakkwato da sauran al’ummarmu da mu ka bar jam’iyyar APC , mu na da dalilan da suka sa mu ka bar wannan jam’iyya, kuma ba jam’iyyar PDP da ku ka sani za mu koma ba’’.
Dan majalisar tarayya daga mazabar Sakkwato ta kudu, Alhaji Ibrahim Abdullahi Danbaba, ya bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labarai a Abuja,kan dalilan da suka sa shi da wasu ‘yan majalisar tarayya daga jihar Sakkwato, suka bar APC, a kwanakin baya.
Alhaji Ibrahim Abdullahi Danbaba, ya ci gaba da cewar, tun a shekara ta 1999, al’ummar jihar Sakkwato,suna jam’iyyar APP ne, saboda kyawawan tsare – tsare na jam’iyyar APP a wancan lokaci, mu ka sami nasarar cin zabe, kuma a wancan lokaci, jam’iyyar da ke jan ragamar gwamnatin tarayya, ba jam’iyyar APP ba ce, ‘amma mu ka sami nasara saboda halayenmu’.
Bayan an kammala mulki a wancan lokaci kuma, a shekara ta 2003, da aka kada kugen zaben wannan shekara, bayan an canza wa APP suna zuwa jam’iyyar ANPP,saboda tsare –tsaren da mu ka yi, wanda mu ka saba yi,da kuma yadda mu ke yi wa al’umma wakilcin da suke samun ribar dimukuradiyya, babu wanda ya sami nasara a jihar Sakkwato sai ‘yan takarar jam’iyyar ANPP a fadin jihar Sakkwato baki daya, kuma a wancan lokaci, a cewar Alhaji Ibrahim Danbaba, babu wani dan takara da ya jingina da Buhari, da tunanin ya ci zabe, sai kowa ya sami nasara a dalilin halinsa da ya shafi alaka da al’ummar da ya ke son ya wakilta.
Dn majalisar tarayya Alhaji Abdullahi Danbaba, ya nunar da cewar, ashekara ta 2007, sai wasu dalilai suka sa suka bar jam’iyyar ANPP, suka koma jam’iyyar PDP,ya ce saboda yadda al’ummar jihar Sakkwato suka yadda da wakilcinsu abin yaba wa da suke yi ma su, ana kada kugen zade, suka sami nasarar takarar da suka shiga, wannan, kamar yadda ya ce , ya nuna al’ummar jihar Sakkwato na tare da wadanda ke tare da su, ako wace jam’iyya, ba su dogara da farin jinin wani wanda ba dan jiharSakkwato ba, a duk zabubbukan da aka yi a baya.Kuma har zuwa shekarata 2011, Alhaji Ibrahim Danbaba ya tabbatar da cewar, ba su bar jam’iyyar PDP ba, suka tsaya suka yi takara, suka kuma sami nasara aduk zabubbukan da suka shiga. Alhaji Ibrahim Abdullahi Danbaba ya tabbatar da cewar, dai –dai da rana daya, ‘yan siyasar jihar Sakkwato,ba su taba tunanin sai sun jingina da Buhari ne za su sami nasara ba, domin a shekara ta 2015, ya ce, sun bar jam’iyyar PDP, suka koma jam’iyyar APC, kamar yadda ya ce, sun shiga jam’iyyar APC ne da al’ummarsu da kuma halayensu, ba da halin wani da wasu ke ganin sai anjingina da shi za a sami nasarar zabe ba.
Alhaji Danbaba, ya nunar da cewar, daukacin al’ummar jihar Sakkwato, a duk lokacin zabe, suna sanya wakilan da suka zaba a sikeli, inda suke yanke hukumcin da sabon gini, gumma su yi sabon yabe, sai su yanke hukumcin sake zaben wakilansu, ba tare da sauraron an zo daga wata jiha, an daga hannunsu ba.
A kuma dalilan da suka sa suka bar jam’iyyar APC zuwa PDP, Alhaji Danbaba ya tabbatar da cewar, sun shafe fiye da shekara biyu suna binhanyoyin da za a yi gyara tare da cika alkawarin da jam’iyyar APC ta yi wa ‘yan Nijeriya, musamman abin da ya shafi cin hanci da karban rashawa da gwamnatin APC ta ce za ta yi yaki da shi, sai har suka fahimci ba za a saurare su ba, a cewarsa an bar shafaffu da mai suna abubuwan da gwamnati ta ce za ta yi yaki da su, sai ya bayar da misalida tsohon sakataren gwamnatin tarayya, na yadda sai da ‘yan majalisar tarayya suka yi tsayuwa irin na mai daka, aka yi ma sa tugar rogo, aka kafa kwamitin binciken matsalar , amma har zuwa yau, wannan batu na aje gefe guda.
Alhaji Danbaba ya kuma ci gaba cewar, hatta duk wanda ya san yadda jam’iyyar APC ta sami nasaraa zaben shekara ta 2015, ya san gwamnoni biyar da suka bar jam’iyyar PDP, suka koma APC, su suka sa jam’iyyar APC ta sami nasara,amma sai aka wayi gari, aka ce, ba za a saurarensuba a duk wasu hidindimu da suka shafi jam’iyyar APC, a karshe, sai wadanda ba a yi yaki da su ba, sai suka zama sahun ma su karban ganiman yakin da aka yi a 2015.
Sauran matsalolin da Alhaji Ibrahim Abdullahi Danbaba ya bayyana da ya ce an yi shakuletin –bangaro da su da suke son a yi gyara, sun hada da kafa kwamitin binciken wasu matsaloli tare da cusa mutanen da ba su cancanta ba,ga matsalolin hukumar man fetur ta kasa, ga matsalolin da suke faruwa a babban bankin Nijeriya, da ya ce sun motsa, amma an ki sauraronsu a gudanar da binciken da yakamata. A karshe, Alhaji Ibrahim Abdullahi Danbaba ya ce babu shakka su da al’ummarsu da suka zabe su a jihar Sakkwato, sun bar Jam’iyyar APC, sun koma jam’iyyar PDP amma ba jam’iyyar PDP da aka sani a yau ba, nan gaba kadan, kamar yadda ya ce sabuwar PDP da suka koma za ta bayyana, kamar yadda ya ce, ita ce, za ta sami nasara a daukacin zabubbukan da za a yi a shekara ta 2019 a Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!