Connect with us

LABARAI

2019: Obasanjo Da Masu Sauya Sheka Ba Su Iya Dakatar Da Buhari Ba –Tinubu

Published

on

agoran Jam’iyyar APC na }asa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce, ba ya tantama Shugaba Buhari ne zai lashe za~en 2019.
Tinubu ya fa]i hakan ne jiya cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas sa’ilin da yake magana da shugabanni da sauran masu ruwa-da-tsaki na Jam’iyyar ta APC reshen Jihar Legas.
Ya ce, Buhari ya tabbatar da cewa shugaba ne shi ya zuwa yanzun duk kuwa da }alubalen da yake ta fuskanta a cikin shugabancin na shi.
Jagoran na Jam’iyyar ta APC, ya yi tir da yawan sukan da tsohon Shugaban }asan nan, Olusegun Obasanjo, yake ta yi wa gwamnatin ta Shugaba Buhari.
Tinubu ya ce, duk sukan da Obasanjon yake yi ba da niyyar alheri ne yake yi ba, kuma ba zai iya hana ‘yan Nijeriya su sake za~an Buhari ]in ba a karo na biyu.
“Shugaba Buhari ya yi }o}ari, ya kuma cancanci a ba shi karo na biyu, za kuma mu goya masa baya ya ci za~en domin shi mutumin mu ne.
“Obasanjo ya yi na shi mulkin, ya kamata ya bar Buhari shi ma ya yi na shi, ya mayar da hankalin shi kan abin da ke gabansa, ba kuma shi ne zai gaya mana wanda za mu za~a ba.
“Yana ]aya daga cikin wa]anda suka jefa }asan nan cikin matsaloli, don bai kafa harsashin abin }warai ba a lokacin da yake shugabancin }asan nan.
Tinubu ya }ara da cewa, ficewar da wasu suka yi daga cikin Jam’iyyar ta APC ba zai hana Buhari ya ci za~e ba.
Tinubu ya ce, za~ukan cike gurbin da aka yi a Jihohin Kogi, Katsina da Bauci wanda duk jam’iyyar ta APC ta lashe su, ‘yar manuniya ce ga abin da zai faru a babban za~en da ke tafe.
“Duk masu son ficewa suna iya ficewa, wannan matsalar su ne. APC kam ko gezau, za kuma su gane kuskuren su a lokacin za~e,” in ji shi. Ya kuma yaba wa Shugaban Jam’iyyar, Adams Oshimhole, ya ce ‘ya’yan jam’iyyar suna yaba ma abin da yake ma jam’iyyar a halin yanzun.
Ya kuma bukaci ‘yan jam’iyyar da su kwa]aitar da al’umma da su mallaki katunan su na za~e, domin da hakan ne ka]ai za su iya samun nasara a 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!