Kotu Ta Umarci Wani Mutum Ya Dinga Biyan Tsohuwar Matarshi 12,000 Duk Wata — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotu Ta Umarci Wani Mutum Ya Dinga Biyan Tsohuwar Matarshi 12,000 Duk Wata

Published

on


Wata kotun shari’a mai zama a Magajin Gari dake jihar kaduna ta umarci wani mutum mai suna Alhassan Abdullahi da ya dinga biyan tsohuwar matarshi Zainab Shu’aibu, Naira 12,000 duk wata a matsayin kudin ciyarwa.

Zainab ta kai karar mijinta ne da ya sake ta sati biyu da suka wuce, alhalin tana da ‘ya mai watanni bakwai a duniya sannan tana da juna-biyu.
‘Ya sake ni bayan yana sane da cewa ina dauke da cikin watanni uku, ina rokon kotu ta umarce shi ya sama min matsugunni da kuma kudin da zan ciyar da diyarmu ‘yar watanni uku. Inji Zainab

Abdullahi dai bai yi musun hukuncin kotun ba, amma yace zai sama mata wajen da zata zauna ita da diyyarsu, sannan zai dinga bata Naira 6000 duk a maimakon 12,000 da kotu ta zartar, amma mai shari’a Dahiru Lawal yace lallai Naira 6000 ya yi kadan ta ciyar da diyyarta, don haka dole ya dinga bata Naira 12,000 sannan ya gaggauta sama mata inda za ta zauna.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!