Mahajjatan Kasar Kanada, Daliban Saudiyya Na Cikin Tasku Sakamakon Rikicin Diflomasiyyar Kasashen Biyu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

Mahajjatan Kasar Kanada, Daliban Saudiyya Na Cikin Tasku Sakamakon Rikicin Diflomasiyyar Kasashen Biyu

Published

on


Maniyyatan kasar Kanada zasu fuskanci tsaikun zuwa da dawowa daga hajjin bana sakamakon bacin alakar diflomasiyya da kasashen biyu suka samu a tsakaninsu, haka ma dalibai ‘yan asalin kasar Saudiyya da suke zaune a Kanada suna ta siyar da kadarorin su don komawa gida Saudiyya kafin wa’adin da kasar Kanada ta saka musu na barin kasar ya kare.

Rikicin dai yana ta kara ruruwa, inda kasar Kanada ta neme taimakon manyan kawayenta irin su Amurka da tarrayar turai don ganin an shawo kan matsalar, Saudiyya ta yanke huldar jakadanci da Kanada sakamakon wani sako na neman a saki fursunonin da ake tsare da su da ministan harkokin waje na kasar kanadan ya yi a shafinsa na Twitter.

Dadin dadawa kasar ta Saudiyya ta tsayar da daukar nauyin daliban kasarta da suke karatun likitanci a jami’o’I daban-daban na kasar Kanada wanda ya tilastawa daliban dawowa gida, har ta kai da dole sai dai daliban su siyar da kadarorin su don komawa gida akan lokaci.

Dalibai kusan 5,100 ne ‘yan asalin Saudiyya suke karatu a makarantun gaba da sakandire a kasar Kanada, a yayin da maniyyata ‘yan kasar Kanada wadanda suka isa Saudiyya don aikin hajjin bana kuma zasu fuskanci tsaiku sosai in suka tashi komawa gida Kanada bayan gama ayyukan hajji.

Amurka wacce babbar kawa ce ga kasashen guda biyu, ta bukaci su sansanta tsakaninsu ta hanyar bin matakan diflomasiyya a yayin da Sakataren Amurka Mike Pompeo suka yi Magana ta waya da yariman Saudiyya wato Muhammad bin Salman.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!