Ramos Ya Caccaki Ronaldo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ramos Ya Caccaki Ronaldo

Published

on


Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Sergio Ramos ya caccaki tsohon dan wasan kungiyar Ronaldo bayan da Ronaldo yayi zargin cewa kan ‘yan wasan kungiyar ta Real Madrid ba a hade yake ba.
Ronaldo yayi wannan zargi ne a jiya a wata tattaunawa da manema labarai a kasar Italiya inda yace kawunan ‘yan wasa da shugabannin kungiyar ba a hade yake ba hakan yasa kowa yake abinda yaga dama.
Sai dai Sergio Ramos, dan kasar Sipaniya, wanda sukayi wasa da Ronaldo a kungiyar ya bayyana cewa kalaman na Ronaldo babu gaskiya aciki kuma kawunan ‘yan wasa shugabanni da magoya baya duk a hade yake.
“Kawunan mu a hade yake babu wata matsala saboda haka bansan inda Ronaldo yasamu wannan labari ba kuma mun samu nasarori da dama tare hakan yana nufin idan kanmu ba a hade yake ba bazamu samu nasarorin ba” in ji Ramos
Yaci gaba da cewa “Babu wani dan wasa dayafi kungiya saboda kowanne dan wasa yana karkashin inuwar kungiya kuma mun samu nasarori tare dashi yanzu kuma duk da yatafi munada karfin gwuiwar cewa zamu cigaba da samun nasara”
Yaci gaba da cewa “Akwai ‘yan wasan da suka buga wasa a kungiyar da yawa kuma suka tafi sannan kuma kungiyar bata tsaya ba taci gaba da lashe kofuna saboda haka hakan bazai canja ba sai dai rashin dan wasa kamar Ronaldo ba karamin nakasu bane ga kungiyar”
Ronaldo dai ya lashe kofuna 15 a kungiyar cikin shekaru 9 da yayi a kungiyar kuma ya buga wasanni 438 sannan ya zura kwallaye 450 sannan ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau hudu a kungiyar.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!