Rundunar ’Yan Sanda Ta Yi Babban Kamu A Zamfara — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Rundunar ’Yan Sanda Ta Yi Babban Kamu A Zamfara

Published

on


Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayana cewa, ta samu nasarar cafke ‘yan ta’adda 20 tare da kwato bindiga 7 daga maboyarsu a wurare daban daban, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Kenneth Ebrimson ya sanar da haka.
Mista Ebrimson ya yi wadannan bayanan ne a tataunawarsa da manema labarai a babban ofishinsu dake Gusa, ya kuma kara da cewa, sashi na musamman da shugaban rndunar ‘yan sanda na kasa ya kafa ne mai suna ‘IGP’s Special Tactical Skuad’ tare da hadin gwiwar jami’an rundunar na jihar suka gudanar da samamen.
“An kama ‘yan ta’addan ne tare da taimakon bayanan sirri kuma nan bad a dade wa za a gabatar da ‘yan ta’adda ga mane labara amma a halin yanzu ga makaman nan da muka kwato a hanun su don kowa ya gani,” inji shi.
Ya kuma kara da cewa, rundunar ‘yan sanda sun ki gabatar da ‘yan ata’addan ne saboda a halin yanzu a na ci gaba gudanar da bincike ne kuma bayyanasu zai iy yi wa binciken da ake yi zagon kasa.
“Muna kira ga al’umma das u taimaka da bamu bayanai don yin haka zai yi matukar tallafa muna wajen cafke ‘yan ta’addan a duk inda suke a fadin jihar, inji shi

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!