Connect with us

HANTSI

Sinawa Na Taimaka Wa Abokai ’Yan Afrika Wajen Warware Matsalar Karancin Hatsi

Published

on

“Matasa manoma ’yan Cote D’ ivoire guda biyu sun ce, a kowace shekara manoman wurin su kan je sansanin gwaje-gwaje a gonakin shinkafa na GUIGUIDOU wanda rukunin masu binciken kimiyyar aikin noma na kasar Sin suka yi, don samun horaswa, kuma sun dawo da wasu sabbin nau’o’in shinkafa. Yanzu suna iya cin shinkafa mai inganci, matakin da ya kyautata zaman rayuwarsu.”——Zhang Yong “Zaman rayuwata a Afrika”

Labari Kan Mista Zhang Yong
Zhang Yong, ma’aikacin kamfanin hadin kan kimiyar tattalin arziki na lardin Liaoning, a shekarar 2012 ya fara zama masanin kimiyyar aikin noma a sansanin gwaje-gwajen gonaki na GUIGUIDOU dake lardin Divo na kasar Cote D’ivoire.
“Gidan Everal na kusa da gonar gwaji ta masanin Basine. Yana aikin gona ne tare da gwanayen Sinawa a rana, sai kuma ya rubuta abubuwan da aka koyar masa lokacin da ya koma gida da dare. Yanzu, yana da ilmin aikin gona sosai, tare da samun kudin shiga da dama, har ma ya yi aure da wata kyakkyawar budurwa. ——Li Xiang: “Abokaina a Burundi”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!