‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum Hudu Da Ake Zargin Masu Safarar Kwayoyi Ne A Gombe — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum Hudu Da Ake Zargin Masu Safarar Kwayoyi Ne A Gombe

Published

on


Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Gombe Mista Shina Olukolu ne ya bada sanarwar cafke wadanda ake zargin dilolin miyagun kwayoyi ne su hudu a yau da safe a garin Gombe.

A cewar kwamishinan an kama mutanen hudu da tarin mugayen kwayoyi, irin kwayoyin da masu aikata mugayen laifukka suke amfani da su, irinsu ake siyarwa yan daban da aka fi sani da ‘Yankalare, wadanda ‘yan siyasa suke amfani da su a matsayin ‘yan dabar siyasa.

‘Ina mai farin cikin shaida muku nasarar cafke manyan dilolin miyagun kwayoyi da muka yi, mun samu wannan nasarar ne ta hanyar amfani da rahotannin sirri da kuma amfani da ma’aikatanmu masu kwarewa wajen ganowa da cafke masu aikata miyagun laifukka, sannan kwayoyin da muka same su da shi irinsu masu aikata muggan laifuka da ‘Yan dabar da aka fi sani da ‘Yan Kalare suke tahamulli da su.’ Inji Olukolu

Kwayoyin sun hada da kwayoyin Valium mai karfin milgram 5 har guda 12,100, kwayoyin Tramol mai karfin milgram 225 guda 900, sai kwayoyin Diazafam mai karfin milgram 5 guda 538, sai Ezzol mai karfin milgram 5 guda 83, akwai kuma kwalaben Codeine da aka haramta sha guda 22 mai karfin milgram 100.

Tuni jami’an ‘yan sanda sun fara shirye-shiryen gudanar da masu laifin a gaban kotu don fuskantar hukuncin da ya dace da su.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!