Zaben 2019; Zan Sake Fasalin Kasa In Na Ci Zabe — Makarfi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Zaben 2019; Zan Sake Fasalin Kasa In Na Ci Zabe — Makarfi

Published

on


Mai fatar a tsayar da shi dan takara karkashin tutar jam’iyyar PDP Ahmed Makarfi ya yi alakwarin, zai sake tsarin fasalin kasar Nijeriya, ga yadda kowa zai ji dadinta, idan aka zabe shi shugaban kasa shekara mai zuwa.

Kamar yadda wani bayanin da ya sanar da manema labarai, Mista Makarfi ya bayyana haka ne ranar Litinin a Asaba, lokacin daya hadu da gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okwa, da kuma wakilan da zasu zo lokacin babban taro na jam’iyyar na hudu ‘yan asalin jihar.

Mista Makarfi dai ya yi gwamnan jihar Kaduna har tsawon shekara takwas, wanda kuma shi ne tsohon shugaban kwamitin riko na jam’iyyar PDP.

Yana daya daga cikin ‘yan takara wadanda suka kai goma sha biyu wadanda kowa yana bukatar a tsayar da shi takara, a zabubbukan 2019.

Ya ce, idan aka zabe shi a shekarar 2019 zai sake tsara Nijeriya, yadda abin zai ma kowa dadi, wannan kuma ya kunshi dukkan wasu abubuwan da suke tallafama ‘yan Nijeriya.

Ya yi kira da a kara fadada yadda ake mulkar jama’a, da kuma kira da gwamnatin tarayya, ta kawo karshen kashe kashen da ake yi da kuma sauran matsalolin da suke damuwar ‘yan Nijeriya.

Mista Makarfi ya bayyana nasarorin daya samu da kuma abubuwan da ya yi ma jam’iyyar PDP, har ma ya ce, shi ne ya fi cancanta  da ya shugabanci Nijeriya.

‘’Ni mai sa’a ne saboda a shekarar 2007 an sa ran cewa nine zan amshi mulki daga hannun tsohon shugaban kasa Obasanjo, amma kuma saboda wani dalili wanda ke baya na lokacin da aka kada kuri’a lokacin zaben fidda gwani, sai aka ba wanda nafi kuri’a.

Ya yi da jam’iyyar ta tsayar da dantakarar da taga ya fi dacewa.

‘’Ba taba bani aikin da ya gagare ne na yi ba, don haka ni ba wani abinda yake tada mani hankali.’’

‘’Ya kamata jam’iyyar PDP ta tsayar da dan takara wanda ya dace, da kuma mutane zasu ji suna son shi, su kuma yi mu’amala da shi, su kuma fito wajen kada kuri’un su da kuma kare su.’’

‘’Idan mika yi abinda mutane ke so zasu iya kasancewa tare damu, kudaden da muke dasu sun isa su sa jam’iyyarmu tayi nasara.’’

‘’Amma kuma idan muka gabatar da dan takarar da bai kamata ba, ba wasu kudaden da zasu sa mu samu nasara, kamar dai yadda ya jaddada.’’

 Da yake magana da ‘yan jarida Mista Okowa ya ce, bayan ya gama ganawa da Mista Makarfi, sai yaji cewar lalle dan takarar, ya san matsalolin Nijeriya.

‘’Idan aka shiga shekarar 2019 Allah kadai ne zai tsara mana abinda yafi dace wa damu a kasarnan, da kuma jam’iyya, babban abin da ya fi kamata mu yi shi ne, mu tabbatar da an gudanar da zabubbukan zaben dan takara kamar yadda doka ta bayyana, da kuma taron kasa’’ kamar dai yadda gwamnan ya ce.

‘’B a wata tantama a kan sauraren Sanata Makarfi, saboda ya gane matsalolin kasar shi, yana da kwatewa, kuma mutum ne mai rikon gaskiya.

 ‘’Kamar yadda kai (Ahmed Makarfi) kake ta tuntubar ‘yan Nijeriya, kana tafiya ta mota, hakan zai sa ka san matsalolin Nijeriya masu yawa, muna kuma fatar zaka ci gaba na zuywa ko wanne sako da lungu na Nijeriya’’

 ‘’ A matsayi na gwamnan jiha zan ci gaba da kasancewa ba mai yawan magana ba, kamar dai yadda gwamnan ya bayyana.’’

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kingley Esiso ya bayyana cewar Makarfi mtum ne mai hakuri da kuma kamala.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!