Connect with us

LABARAI

Da Alkawarin Boge APC Ta Yaudari ‘Yan Nijeriya A 2015 – Gwamna Dankwambo

Published

on

Gwaman jihar Gombe Alhaji Ibrahim Dankwambo kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya bayyana cewar  yaudara ‘yan Nijeriya aka yi kafin  zaben 2015 ta hanyar yi masu karya da sunan canjin da a yau ya jefa su a cikin kuncin rayuwa..

Dankwambo ya bayyana hakan ne jiya a garin  Ado-Ekiti da ke cikin jihar Ekiti a lokacin da ya gana da wakilai masu zaben dan takarar shugaban kasa a PDP da ke jihar.

Acewar sa kamata ya yi ‘yan Nijeriya su fi yadda suke a karkashin mulkin APC amma sai suka yi gaggawa wajen neman canji a 2015 wadda jam’iyyar ta yi masu alkawari da sunan canji, yana mai karwa da cewa“dole za mu tabbatar da tsaro, farfado da  tattalin arziki ba wai kashe shi ba”.

Akan zaben kujerar gwamna da aka gudannar a kwanan baya a jihar ta Ekiti kuwa ya ce, za su kalubalanci zaben a Kotu.

A nashi jawabin gwamnan Jahar Ayodele Fayose ya bayyana cewa ‘ya’yan PDP a jihar za su dauki matsaya a kan wanda za su zaba a lokacin zaben na fidda gwani na jami’yyar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!