Rashin Zaman Majalisa Na Haifar Da Fargabar Gudanar Da Zaben 2019 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Rashin Zaman Majalisa Na Haifar Da Fargabar Gudanar Da Zaben 2019

Published

on


Akwai damuwa da tararrabin gudanar da babban zaben 2019 a kan lokacin da aka tsara gudanar da shi, kasantuwan tabbacin cewa Majalisun tarayya ba za su yi wani zama ba a nan kusa domin su duba kasafin kudin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta gabatar da kuma sauran hukumomin tsaro.

Shugabannin Majalisun sun yi wani taro a makon da ya gabata inda suka cimma yarjejeniyar kiran wani zaman majalisun na musamman a ranar Laraba ko jiya Alhamis, domin su duba kasafin kudin hukumar zaben da ma wasu mahimman al’amura da suka shafi kasa, bayan taron da suka yi da shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu, a ranar Alhamis ta makon da ya gabata. Amma sai akasin hakan ya biyo bayan waccan sanarwar zaman majalisar na wannan makon, inda Shugaban majalisar ta Dattawa, Bukola Saraki, da Kakakin majalisar wakilai ta kasa,

Yakubu Dogara, a jiya suka bayar da sanarwar cewa, ba a sanya wata ranar kiran zaman majalisun ba domin su duba kasafin kudin hukumar zaben.

A cewar su, hakan ya faru ne kasantuwan gazawan zaman da aka shirya kwamitocin duba dokokin zabe na majalisun biyu da aka shirya za su yi zaman hadin gwiwa tare da jami’an hukumar zaben da ma jami’an kwamitocin hukumomin duba kasafin kudi da na basuka, ba su sami yin zaman ba kamar yadda aka shirya tun da farko. Shugabannin majalisun biyu sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da masu taimaka masu kan harkokin yada labarai, Yusuph Olaniyonu da Turaki Hassan suka sanya wa hannu.

Sanarwar ta yi nu ni da cewa, “Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Yakubu Dogara, sun umurce mu da mu sanar da dukkanin wakilan majalisun biyu da ma al’umman kasa cewa, har yanzun ba a sanya sabuwar ranar da majalisun za su zauna ba domin su duba kasafin kudin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta gabatar kan babban zaben shekarar 2019, kamar yadda Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aike wa majalisun a ranar 17 ga watan Yuli 2018.

Shugabannin majalisun biyu sun zauna sun kuma cimma yarjejeniyan su kira zaman majalisun na musamman a cikin wannan makon, wanda taron hadin gwiwa na kwamitocin duba harkokin zabe na majalisun biyu da jami’an hukumar zaben zai gabace shi kafin, ko kuma a ranar Litinin 13 ga watan Agusta 2018. “Wannan kwamitin na hadin gwiwa ana kuma sa ran zai yi zama da kwamitocin majalisun kan kasafin kudi da na basuka, wanda daga nan ne za su gabatar wa da majalisun sakamakon zaman na su guda biyu.

“Sai dai kuma, wadannan kwamitocin ba su sami yin zaman ba, wanda hakan ya sanya majalisun na tarraya biyu ba za su kira zaman ba, kasantuwan ko sun zauna ba wani abin da za su duba. Don haka yanzun, har sai ranar da wadannan kwamitocin suka zauna suka gabatar wa da majalisun tabbataccen rahoton da majalisun biyu za su duba, bisa hakan, ba bukatar katse wa wakilan majalisun biyu hutun su, musamman ma wadanda suka ta fi Saudi Arabiyya domin yin ayyukan Umrah da Hajji.”

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!