Yau Ake Sa Ran Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Yau Ake Sa Ran Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya

Published

on


A yau ne Hukumar Kula da Alhazai ta Nijeriya ta k uduri aniyar kammala jigilar maniyyatan Nijeriya, kamar yadda ta tsara tun farkon fara jigilar.

Ya zuwa shekaran jiya Hukumar ta NAHCON ta yi jigilar sama da maniyyata 35,000 a jirage 90 da suka tashi daga Nijeriya zuwa K asar Saudiyya don sauke farali, kamar yadda sashen fitar da bayanai na Hukumar ya fitar a shekaran jiya.

Sashen wanda ke k ark ashin hukumar NAHCON ya bayyana cewa, ya na da tsarin taskace duk wani jigilar maniyyata da aka gudanar daga Nijeriya zuwa Saudiyya.

Jigilar Maniyyatan Nijeriya a bana yana ci gaba da gudana ne ta hanyar yin amfani da jirage biyu na gida; Jirgin MAD da MEDBIEW. Sai kuma jirgin K asar Saudiyya guda daya wato FLYNAS.

Za a fara gudanar da aikin hajjin na bana ne dai a ranar Lahadi mai zuwa, inda za a fara da jigilar maniyyata daga masaukansu a Makkah zuwa Rumfunan da aka tanada a Muna.

Ranar Litinin ne Maniyyata za su hallara a filin Arfa, inda za su kwashe ranar gabadayanta wurin salloli da addu’o’i.

Daga Arfah ne za a yi jigilar Maniyyatan zuwa Muzdalifa, wani fili dake tsakanin Arfah da Muna, inda a can ne za su kwana.

A na sa ran cewa Maniyyata miliyan biyu da za su kasance a hajjin bana za su gudanar da ibadar jifar shaidan a Jamrat.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!