AMBALIYAR RUWA — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

AMBALIYAR RUWA

Published

on


Sakamakon binciken masana ya nuna cewa bana za a iya samun ambaliyar ruwa awurare da dama a kowanne bangare na Nijeriya wanda hakan ba karamin nakasu zai jawo wa kasa ba, hakan baya rasa nasaba da mamakon ruwan sama da muke gani a damunar bana, wanda a yanzu haka a jahohi kamar su Katsina da Sakkwato da ma Kano sun fara fuskantar barazana daga ruwan sama da ke nuni ko tabbatar da hasashen masana dangane da mumunar annoba ta amabliya.

Wannan kuma yana faruwa ne sakamakon dalilai mabambata, kama da canji yanayi da dumamar yanayi da toshe magudanan ruwa da fasa dam da rashin kananan maragar ruwa  da fashewa dam sakamakon yawan ruwan sama da sauran dalilai mabambanta:

Idan muka duba yawancin dalilalan da suka gabata za mu gane cewa yawancin matsalar na afkuwa sakamakon ayyukan son zuciya na bil’adama domin biyan bukatar kansa don bunkasa muhallinsa :

Toshe magudana ruwa sakamakon zub da shara barkatai da jama’a ke yi a manyan biranenmu, hakan na sanya hanyoyin ruwa su toshe wanda hakan ba karamar illa yake jawo wa muhallinmu da kuma taba lafiyarmu domin yawancin cututtukan da suke damun mazauna birane ba sa rasa nasaba da wannan dabi’a ta hanawa ruwa hanyarsa wanda hakan ne yake jawo cututtuka kamar su maleriya sakamakon tara sauro da kwatocinmu ke yi a cikin ledoji da robobi wanda su ne mafiyan shara da ke taruwa.

Fashewa Dam: Sakamakon yawan ruwan sama da ake samu a wannan lokaci da toshe hanyar maragar ruwa a yawancin dam-dam dinmu na jawo ruwa ya nema wa kansa hanya ta karfi wanda hakan na jawo wa manoma asara ta dimbin dukiya da asarar kasar noma a wasu bangarorin kasar nan. Dam  ya kasancewa hanyar bunkasa tattalin arziki da samar da wurin kiwo ga dabbobi da noma ga dimbin jama’a Nijeriya, sakamakon bude hanyoyi da manoma suke yi domin jan ruwa a gonakinsu hakan na zama hanyar ambaliya haka kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya na jawo ambaliyar ruwa a wadansu wurare .

 

Canji Yanayi : Sakamakon narkewar kankara a teku hakan na jawo karuwar yawan ruwan da ke gudana a rafuka har ya fi karfin dauka wannan rafi wanda sakamakon hakan ke jawo ambaliya a gurare da dama kuma hakan na jawo asarar dukiyoyi da rayukan jama’a, a bana jihar Katsina da ke Arewacin Nijeriya tasha fama da matsalar ambaliyar ruwan sama wanda hakan ya jawo rasa dukiyoyi da rayukan jama’a. Hakama a makwabciyar Nijeriya wato a birnin Zinder ta kasar Nijar an sami ambaliya ruwa a bana wanda aka rasa rayuka da dukiyoyi.

A Kwanakin baya an sami ambaliya a wasu wuraren inda sakamako haka ya hallaka mutane da dama a garin Suleja da ke jihar Neja. Jihohin Legas, da Oyo da Sakkwato da Zamfara da Binuwai da Adamawa da Neja da Kwara da Ogun duk suna cikin wadanda ambaliya na iya rutsawa da su. Inda shugaban Hukumar NIMET mai kula da yanayi Farfesa Sani Mashi ya ce ruwan sama zai ci gaba da yin gyara a wasu wuraren da ba su yi wani tanadi ba domin ambaliya.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!