Connect with us

LABARAI

An Tsaurara Hana Zuba Shara A Mugudanan Ruwa A Damaturu

Published

on

Kwamitin kula da tsaftace muhalli na jihar Yobe ya gargadi magidantan da ke da dabi’ar zuba shara a magudanan ruwa da su bari tun da girma da arziki, don duk wanda aka kama shi da wannan laifi za a hukunta shi.

Mataimakin gwamnan jihar, Abubakar Ali, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tsaftace muhalli ne ya yi wannan gargadin lokacin kaddamar da kwamitin da zai binciki dalilin ambaliyar ruwa wanda ya yi sanadiyyar rushewar gidaje da kuma asarar dukiya mai yawan gaske a Damaturu.

Mataimakin gwamnan ya ce, gwamnatin jihar ta kashe makudan kudade wajen yin magudanan ruwa amma wasu mutane marasa kishi na zuba shara a ciki, wanda hakan ta toshe su kuma shi ne dalilin afkuwar ambaliyar ruwan da ta faru wadda mutane da dama suka rasa muhallinsu.

Haka kuma ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar za ta yi amfani da rahoton da kwamitin zai bayar, wanda ake fatan ya kawo karshen sake afkuwar irin haka nan gaba.

Shi ma a nasa jawabin babban manajan hukumar tsaftace muhalli ta jihar, Idi Wadina, cewa ya yi, “Kuma za mu ci gaba da share magudanan ruwa yadda ruwa zai wuce cikin sauki da dukkan wani abu da zai kawo cikas wajen tafiyar ruwan a dukkan fadin wannan jiha.

“Muna gargadi ga muatanen da ke jibge shara a magudanan ruwansu suna jiran sai mun zo mu yashe musu, ba ma sa tunanin lafiyarsu, har ma suna zargin gwamnati idan ambaliayar ruwa ta faru, da su gaggauta barin wannan hali mara kyau “,in ji shi.

Wadina  ya kuma ce ambaliyar ruwan da ta faru a Damaturu, ambaliya ce wadda dan shekara 20 ma bai tada ganin irin ta ba.

Saboda haka sai ya bukaci dukkan wadanda suka san sun yi gini a kan magudanan ruwa da su gaggauta rushe su tun kafin Hukuma ta zo ta kawar da su,  domin kuwa gwamnati ba za ta amince da yin hana ba, saboda hakan na cutar da al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!