Bale Ba Zai Iya Maye Gurbin Ronaldo Ba --- Isco — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Bale Ba Zai Iya Maye Gurbin Ronaldo Ba — Isco

Published

on


Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Isco, ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Gareth Bale, bazai iya maye gurbin Ronaldo ba a kungiyar sakamakon ba shi da wasu abubuwa da Ronaldo yake dasu.

Isco ya bayyana hakane bayan tashi daga wasan da kungiyar Atletico Madrid ta dokesu daci 4-2 a wasan karshe nacin kofin Super Cup da aka buga a kasar Estonia.

‘yan wasa Karim Benzema da Ramos ne dai suka jefa kwallaye a ragar Atletico Madrid kuma Bale ne ya bugowa Benzema ya zura kwallon ta farko da kungiyar taci sai dai bai zura kwallo a wasan ba.

Sai dai Isco ya bayyana cewa yayi zaton Bale zai buga wasa wanda yafi wanda yabuga a wasan amma kuma bai buga ba hakan yasa shakku a  zuciyarsa na cewa dan wasan dan kasar Wales bazai iya maye shahararren dan wasa Ronaldo ba.

Sai dai kafin wasan na ranar Laraba, mai koyar da ‘yan wasan kungiyar, Julian Lepatugui, ya bayyana cewa yadda Bale ya shiryawa wasan ya burgeshi kuma yana ganin a shirye dan wasan yake daya maye gurbin na Ronaldo.

Real Madrid dai ta buga wasan ne da kwararrun ‘yan wasanta gaba daya kuma ranar Lahadi kungiyar zata fara buga wasanta na farko na gasar laliga da kungiyar Getafe a filin wasa na Santiago.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!