Connect with us

WASANNI

Ramos Ya Gargadi Barcelona Da Atletico Madrid

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Sergio Ramos ya bayyana cewa rashin nasarar da sukayi a hannun kungiyar Atletico Madrid a wasan karshe na cin kofin Super Cup bazai karyar musu da jiki ba kuma zasu sake dagewa.

Real Madrid tafara kakar wasa batare da dan wasa Cristiano Romaldo ba wanda yakoma Jubentus da kuma Zidane, wanda yabar aikin koyar da kungiyar bayan ya jagorance su lashe kofin zakarun turai a kakar wasan data gabata.

Sai dai tun bayan tafiyar Ronaldo ake ta danganta manyan ‘yan wasa da komawa kungiyar domin maye gurbinsa ciki kuwa har da dan wasan Chelsea, Edin Hazard da Neymar na PSG da takwaransa na PSG din, Kylian Mbappe.

“Zamu cigaba da bugawa Real Madrid wasa domin samun nasara kuma zamu sake saka farin ciki a zuciyoyin magoya bayanmu na duniya sannan kuma yanzu muka fara samun nasara domin Real Madrid a zuciyar mu take” in ji Ramos

Yaci gaba da cewa “Kungiyoyin da suke kasar Sipaniya musamman manyan kungiyoyi yakamata su sake sabon shiri domin wannan kakar da karfinmu zamu dawo domin lashe kofin laliga”

Rashin nasarar da Real Madrid tayi a hannun Atletico Madrid yasa takasa kasancewa kungiya ta farko da zata lashe kofin sau ukua  jere bayan ta lashe sau biyu a baya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!