Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Shirya Kai TayinKAI Fam Miliyan 120 Domin Siyan Hazard

Published

on

Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya tsaf domin sake kai tayin kudin daya kai fam miliyan 180 ga kungiyar kwallon kafa ta Chelsea domin cinikin Edin Hazard.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta dade tana zawarcin dan wasan wanda kungiyar take ganin zai iya maye gurbin dan wasa Cristianao Ronaldo a kungiyar sakamakon shahararren dan wasan yabar kungiyar zuwa Jubentus.

Hazard, mai shekaru 27 a duniya yaki amincewa da sabon kwantaragin da kungiyar Chelsea tayi masa na shekara hudu inda aka bayyana cewa dan wasan yagaji da zama a kungiyar kuma yanason ya gwada nasararsa a kungiyar Real Madrid.

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane ya dade yana zawarcin dan wasan tun yana mataimakin mai koyarwa a kungiyar ta Real Madrid karkashin jagorancin Carlo Ancelotti dan kasar italiya.

Sai dai kungiyar Chelsea batason rabuwa da dan wasan nata wanda yana daya daga cikin manyan yan wasan kungiyar a daidai wannan lokaci kuma tuni mai koyar da ‘yan wasan kungiyar, Mauricio Sarri ya bayyana cewa bai kamata kungiyar ta siyar da dan wasan ba indai kungiyar tanason taci gaba da lashe kofuna.

Tuni aka bayyana cewa dan wasan ya nuna sha’awarsa ta komawa Real Madrid tun bayan kammala gasar cin kofin duniya inda yace yana bukatar sabuwar kungiya domin ya gwada kwallonsa sai dai abune mai wahala kungiyar ta siyar dashi bayan da a satin daya gabata aka rufe kasuwar siyan ‘yan wasa a kasar Ingila

 

Ana saran kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata kai tayin kudi fam miliyan 180 a tayin farko domin a fara cinikin sai dai ana tunanin dan wasan zai kai kusan fam miliyan 200 idan har Chelsea za ta amince da siyar da dan wasan nata dan asalin kasar Belgium.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!