Connect with us

Uncategorized

‘Yan sanda Sun Sake Kama Wadanda Ake Zargi Da Kashe Manajan Gidan Man Kams

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewar karin wadanda ake zargi da kisan Manajan gidan man Kams biyu sun sake fada wa hanunsu.

Wadanda ake zargin dai sun kai farmaki ne a gidan man a shekarar da ta gabata inda suka yi fashi hadi da kashe Manajan gidan man a lokacin da ya yi yunkurin ba su matsala a kokarinsu na yin fashin a gidan man, lamarin da ya janyo ajalinsa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Kamal Datti Abubakar shine ya shaida hakan a cikin wata kwafin sanarwa da ya raba a jiya, ya ce tun bayan kisan, sun cafke wasu da har suka kai su kotu, a yayin da suka ci gaba da zurfafa bincikensu kan lamarin.

Ya ce; “Idan za ku iya tunawa a ranar 16/12/2017 mun baje muku wasu da muka kama masu suna Oyeka Dabid 32, Oyeka Okeke 34, Grace Otapa 24, da kuma   Happy Henry 32 wadanda muka kame su hade da gurfanar da su a gaban kuliya kan zargin yin fashi da makami da kuma kashe Majanan wani gidan man KAMS UNIBERSAL CONCEPT LTD da ke kan itin Jos a cikin garin Bauchi.

“Bincikenmu ya ci gaba da zafafa domin ganin dukkanin masu hanu kan wannan kisan mun taso keyarsu hade da gurfanar da su a gaban kuliya,” A cewar DSP

Datti ya shaida cewar a bisa haka ne rundunarsu da ke aiki a kan masu fashi da makami suka sake samun nasarar cafko Julius Haruna wanda aka fi sani da ‘Don Jazzy’ mai shekaru 32 mazaunin Kongo Rosha a jihar Filato da kuma Babangida Abdulazeez da ake kira da Rati mazaunin unguwar Igbo Kuarters Bauchi bisa hadin kai kan wannan fashin da kuma kisan Manajan gidan man, a bisa haka ne ya shaida cewar suma za su gurfanar da su a gaban shari’ar.

DSP Kamal ya bayyana cewar nan bada jimawa ba ne za su gurfanar da su a gaban kuliya domin ci gaba da fuskantar shari’a daidai da laifinsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!