Real Madrid Za Ta Biya Fam Miliyan 35 Idan Har Tana Son James Rodriguez Ya Koma Gida — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Real Madrid Za Ta Biya Fam Miliyan 35 Idan Har Tana Son James Rodriguez Ya Koma Gida

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana tunanin biyan fam miliyan 35 ga kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen idan har tanason ta sake mayar da dan wasanta James Rodriguez wanda yake zaman aro a Munich din.

A kakar wasan data gabata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta amince ta bada dan wasan nata aro zuwa Bayern Munchen har na tsawon shekaru biyu bayan da dan wasan ya bukaci hakan sakamakon baya samun buga wasanni a  lokacin tsohon kociyan kungiyar Zidane.

Acikin ‘yar jejeniyar da kungiyoyin suka kulla a shekarar data gabata dan wasan zai zauna shekara biyu a kungiyar ta Bayern Munchen amma kuma idan Real Madrid tanason ta mayar da dan wasan nata bayan shekara daya sai ta biya fam miliyan 35.

Tun bayan tafiyar Cristiano Ronaldo zuwa Juventus  Real Madrid take zawarcin dan wasan gaba wanda zai maye mata gurbinsa amma kuma har yanzu bata samu ba bayan da Hazard yace bazai koma kungiyar ba hakan yasa Real Madrid tafara tunanin biyan kudi domin dawo da dan wasanta.

Kungiyar dai tana tunanin biyan kudin idan har taga ‘yan wasan da take nema bata samu ba kuma kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen itama ta bayyana cewa a shirye take data amince da cinikin.

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar ta Real Madrid, Julian Lepatugui dai ya bayyana cewa akwai bukatar siyan babban dan wasa amma kuma idan kungiyar bata samu ba yana farin ciki da ‘yan wasan da yake dasu.

Advertisement
Click to comment

labarai