Shehu Sani Da ‘Yan Takarar APC 14 Sun Ce Basu Amince Da Zaben ‘Yan Takarar Jam’iyyarsu Ba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Shehu Sani Da ‘Yan Takarar APC 14 Sun Ce Basu Amince Da Zaben ‘Yan Takarar Jam’iyyarsu Ba

Published

on


Sanata Shehu Sani da wasu ‘yan takarar su 14 a inuwar jam’iyyar APC ta jihar Kaduna sun ce ba su yi amana da tsarin tsayar da ‘yan takara ta hanyar zabin wasu su kadai ba a jam’iyyar.

Shehu Sani da sauran ‘yan takarar sun rubuta wa uwar jam’iyyar ta kasa takardar koke inda suka bukaci a yi zaben kai tsaye ba sabanin haka ba,  wanda kwamitin gudanarwar jam’iyyar na jiha ya fitar da sanarwar aikin da da shi don tsayar da ‘yan takara.

Su Shehu Sani suna ganin wannan matakin ya saba da akidar da ake kallon shugaban kasa Buhari da ita, ta yaki da cin hanci da rashawa a duk fadin kasar nan, haka ma ya saba da taken jam’iyyar na canji.

‘Mu kira da uwar jam’iyyar mu tabbatar ta tsaida wannan shiri na zabe ta bayan fage, kuma lallai wannan matakin bai dace da dimokradiyya ba, sannan ba abinda zai haifar sai rashawa da siyan kuri’a, don haka dole a dauki matakin ganin an tsayar da wannan shirin.’ Inji su

‘Yan takarar sun hada da Shehu Sani mai neman tazarcen kujerar Sanata a Kaduna ta tsakiya,  halal Falal dan takarar kujerar gwamna, Muhammad Sani Dan takarar kujerar Sanata Kaduna ta tsakiya, Aliyu Silver mai takarar Sanata Kaduna ta arewa, Rufa’i Chanchangi dan takarar majalisar wakilai,

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!