Connect with us

WASANNI

Ban Taba Tunanin Barin Real Madrid Ba

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Marco Asensio ya bayyana cewa bai taba tunanin barin kungiyar ba domin komawa wata kungiyar saboda yana jin dadin zamansa a kungiyar.

Asensio ya zura kwallaye 21 cikin wasanni 95 daya buga a kungiyar tun bayan komawarsa Real Madrid din daga kungiyar Mallorca ciki har da kwallaye 11 cikin wasanni daya bugawa kungiyar a kakar wasan data gabata.

A kakar wasan data gabata an danganta dan wasan da komawa gasar firimiya inda aka ce kungiyoyin Manchester United da Manchester City da Liverpool suna zawarcinsa sai dai daga baya Real Madrid tace dan wasanta bana siyarwa bane.

Sai dai dan wasan ya bayyana cewa bai taba bayyana ko tunanin barin kungiyar ba bayan da tsohon kociyan kungiyar Zinadine Zidane yabar kungiyar kwanaki biyar bayan ya jagoranci kungiyar ta lashe kofin zakarun turai.

“Ban taba tunanin barin kungiya taba saboda babu kamarta duk duniya saboda haka duk inda zanje a duniya zanje inda bai kai Real Madrid bane kuma bana fatan ci baya a rayuwa ta” Inji Asensio, wanda dan asalin kasar Sipaniya ne.

Dan wasan dai ya zura kwallo daya sannan ya taimaka an zura kwallaye hudu a wasan rukuni rukuni na nahiyar turai na kasashe da Sipaniya ta lallasa kasar Croatia.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!